Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria

Gidan kallon kwallo a Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gidajen kallo na da farin jini sosai a Najeriya

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta ce za ta girmama magoya bayanta da suka mutu bayan turken wutar lantarki ya fada kansu a lokacin da suke kallon wasa a birnin Calabar na jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, United ta ce 'yan wasanta za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi "domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria."

Hukumomi sun ce mutum bakwai ne suka mutu a lokacin da lamarin ya faru, yayin da wasu goma suka samu raunuka.

Sai dai wasu da suka shaida lamarin, sun fada wa BBC cewa adadin ya fi haka, yayin da kafafen yada labarai na cikin gida ke cewa mutum 30 ne suka mutu.

Lamarin ya faru lokacin da jama'a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya "kadu kwarai" da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama'a.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption 'Yan wasan United za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria"

Labarai masu alaka