An kama shinkafar waje ta miliyan hudu

Shinkafar Ebonyi
Image caption Manoman shinkafa suna kokawa da irin tasirin da fasa kaurin shinkafa ke yi kan harkarsu.

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya da ke kula da yankin jihar Kano da Jigawa ta ce ta kama wata tirela makare da shinka `yar waje da aka yi yunkurin fasa-kwaurinta zuwa Najeriya.

Kwanturolan yankin, Matias Abutu Onoja yace shinkafar kudinta ya kai fiye da naira miliyon hudu. A cewarsa an kama motar ne a kusa da Dutse hedikwatar jihar Jigawa.

Hukumar ta yi wannan kamun ne kwana biyu bayan zargin da kungiyar masu sarrafa shinkafa ta yi cewa ana fasa-kwaaurin shinkafa ta wasu iyakokin Najeriya da ke tudu.

Ko da wakilin BBC ya tambayi Konturolan kan me ya sa kamun na su na zuwa kwana biyu bayan masu noman shinkafa suka fara korafi kan fasa kaurin, sai ya ce su na kamun ne in har sun gano an shigo da kayan waje ba bisa ka'ida ba.

Ya ce hukumar tana neman masu shinkafar domin ta hukunta su.

Wannan na zuwa ne a lokacin da manoma ke kukan cewar fasa kaurin shinkafa na yi wa harkar su lahani.

Labarai masu alaka