Ba zan yi takarar shugaban Amurka ba - Michelle Obama

Michelle Obama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Michelle Obama ta kira Trump da cewa "sabon shugaban kasa"

Mai dakin tsohon shugaban kasar Amurka Michelle Obama ta nuna yiwuwar ba za ta tsaya takarar shugabancin kasar ba a karon farko da ta fito bainar jama'a tun bayan fita daga fadar White House.

Mrs Obama, wacce ta fice daga ofis a lokacin da farin jinta a idon 'yan kasar ya kai kashi 68 cikin (fiye da kashi goma kan mijinta) ta ce "siyasa na da matukar wuya."

Ta bayyana haka ne a Orlando kwana kadan bayan Obama ya fito bainar jama'a a Jami'ar birnin Chicago karon farko tun bayan saukarsa.

"Komai zai rika tafiya daidai amma da ka soma takara za a yi ta sukarka."

Ta ce hakan zai bai wa iyalinta wahala, tana mai cewa: "Ba zan bari 'ya'yana su sake fuskantar matsala ba, saboda idan mutum yana takara ba shi kadai lamarin ke shafa ba har da iyalinka ."

Sai dai Michelle Obama ta ce bautawa al'uma shi ne kan gaba a rayuwarta.

Labarai masu alaka