An sallami jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu daga kurkuku

Nnamdi Kanu Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Daya daga cikin sharudan ba da balin Nnamdi Kanu shi kar ya yi zanga-zanga

An saki jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga gidan yari bayan ya cika sharudan da wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta sanya masa.

A ranar Talata ne dai kotun, karkashin mai shari'a Binta Nyako, ta bayar da belin Mr Kanu saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sai dai ta sanya masa sharuda, wadanda suka hada da cewa ya gabatar da mutum uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari'ar ta ce ba a yarda a gan shi a cikin taron jama'ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa "kar ya yi hira da 'yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga".

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari'ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutum uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

Labarai masu alaka