An ɗaure angon da ya yi wa baƙuwa fyaɗe

A convict Derry Flynn McCann Hakkin mallakar hoto MET POLICE
Image caption Derry Flynn McCann ya amsa laifi kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma yin fashi

An yanke wa wani ango hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda yi wa wata baƙuwa fyaɗe sa'o'i kafin ɗaura masa aure da abokiyar zamansa mai juna biyu.

A ranar 13 ga watan Janairu ne, Derry Flynn McCann ɗan shekara 28, ya auka wa wadda ya yi wa fyaɗe na tsawon sa'a biyu a yankin Hackney da ke gabashin London.

Kwanan nan aka sako shi daga gidan yari saboda aikata irin wannan laifi.

Wani alƙali a kotun Snaresbrook ya bayyana Derry McCann a matsayin "wani ibilishi" kuma ya ce sai ya yi zaman gidan yari na aƙalla shekara 9.

Yayin wannan fyaɗe na tsawon lokaci, McCann ya yi duka kuma ya muzanta wannan mata sannan ya ɗauki hotunanta ya sace mata waya.

A zaman da kotun ta yi cikin watan Maris a baya, Derry McCann na unguwar Hackney ya amsa laifinsa kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma wata tuhumar kan cin zarafin 'ya mace gami da tuhuma ɗaya kan aikata fashi.

Masu bincike sun yi imani cewa Derry ya biyo wata mata ce amma sai ta ɓace masa don haka sai ya auka wa wadda abin ya faru a kanta.

An fahimta cewa ko a shekara ta 2006 ma an ɗaure McCann kan aikata wani dogon fyaɗe da ya yi.

Labarai masu alaka