Me ya sa APC ta kasa zama dunƙulalliyar jam'iyya?

Kakakin APC ya ce kan 'yan jam'iyyar a haɗe yake Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kakakin APC ya ce kan 'yan jam'iyyar a haɗe yake

Tun bayan da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta lashe zaɓen shekarar 2015, masana harkokin siyasa ke cewa ta yi abin da Hausawa ke cewa samun duniyar ɗan tsako: ba samun ba, inda za a zauna a ci.

Sun kuwa bayyana haka ne ganin cewa, ba kamar jam'iyyar PDP ba wacce aka kafa da zummar bin turbar dimokraɗiyya ba, akasarin 'yan jam'iyyar APC haɗin gambiza ne: 'yan tsohuwar jam'iyyar CPC irin su Shugaba Muhammadu Buhari, da na tsohuwar jam'iyyar AC, kamar su Bola Tinubu da kuma waɗanda zama a jam'iyyar PDP ya yi wa zafi, irinsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

A cewar Dr Abubakar Kari, na Sashen koyar da kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja, babban ƙalubalen da APC ke fuskanta shi ne na rashin haɗin kan ɓangarori daban-daban da suka kafa ta.

Ya shaida min cewa "Babbar matsalar jam'iyyar APC ita ce har yanzu ba ta zama jam'iyya ta dunƙule wuri ɗaya ba; har yanzu gungu-gungu na 'yan jam'iyyu daban-daban ne irinsu tsohuwar jam'iyyar ACN da CPC da kuma tsohuwar PDP. Babu wanda yake kallon APC a matsayin jam'iyya, kuma hakan ne ya sa ake fuskantar manyan matsaloli a jam'iyyar."

Shi ma Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma ƙusa a jam'iyyar PDP mai hamayya, ya gaya wa BBC cewa APC jam'iyya ce ta mutanen da suka yi fushi, waɗanda ba su da wata kyakkyawar manufa sai dai "cin mutuncin jama'a."

Sai dai kakakin jam'iyyar ta APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya shaida min cewa: "APC jam'iyya ɗaya ce da ke da manufa guda: kawo ci gaba a Najeriya. Haka kuma kan 'yan jam'iyyar a haɗe yake, ko da yake ba za a rasa 'yar rashin jituwa tsakanin wasu ba, amma haka mulkin dimokraɗiyya ya gada."

Wani babban batu da ya nuna cewa zama ake irin na gidan haya a APC shi ne yadda tun da aka zo zaɓen shugabannin majalisar dokokin tarayya 'yan jam'iyyar ta APC suka ƙi zaɓar mutanen da jam'iyyar ta tsayar, abin da Dr Kari ya ce ya dasa dambar rashin jituwa tsakanin manyan 'yan jam'iyyar.

Wasu dai na ganin hakan ba ya rasa nasaba da alwashin da Shugaba Buhari ya sha ba na barin kowanne bangare ya ci gashin kansa ba tare da katsalandan ba.

Sai dai wasu masu sharhin na ganin karan dimokraɗiyyar Najeriya bai kai tsaikon da shugaban ƙasa zai ƙi sanya hannu a sha'anin wasu ɓangarorin ba, musamman ganin cewa duk abin da ya faru a wani ɓangaren, kai-tsaye zai shafi wasu ɓangarorin.

Da alama masu wannan ra'ayi na da hujja domin kuwa shurun da Shugaba Buhari ya yi kan al'amuran da ke faruwa a majalisar dokoki da kuma jam'iyyarsa ta APC har sai da lokaci ya kusa ƙurewa ya sa al'amura sun riƙa rincaɓewa a ƙasar.

An yi ta samun rigingimu tsakanin shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun da wasu jiga-jiganta irinsu Bola Ahmed Tinubu a kan zaɓukan jihohin Kogi da Ondo, lamarin da ya har ya kai su yin fito-na-fito a kafafen watsa labaran ƙasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Buhari ya kayar da Atiku a zaben fitar da gwani na APC

Shi kansa tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar sai da ya tsoma baki a cikin rigimar inda ya nuna goyon bayansa ga Mr Tinubu.

Bayan faruwar wannan lamari ne, wanda har yanzu wasu ke ganin tsugune ba ta ƙare a kansa ba, wasu rahotanni suka nuna cewa manyan jami'an na APC cikinsu har da shi Ahmed Tinubun da Atiku Abubakar na shirin kafa sabuwar babbar jam'iyya, zargin da suka musanta.

Babban taro ya gagara

A can jihar Adamawa ma, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, an ambato wasu shugabannin jam'iyyar APC na cewa babu wanda za su mara wa baya a zaben 2019 idan ba Atiku Abubakar ba.

Kazalika wasu 'yan kasar na ganin hatsaniyar da ke faruwa tsakanin 'yan majalisar dattawa da ɓangaren zartarwa kan wasu batutuwa na da nasaba da hanƙoron da shugaban majalisar Bukola Saraki ke yi na tsayawa takara a 2019, ko da yake ya shaida wa BBC cewa "yanzu ba lokacin siyasa ba ne."

Sau da dama APC na shirya gudanar da babban taro amma hakan ya ci tura.

Ko da a baya bayan nan, an shirya yin taron ranar 24 zuwa 25 ga watan nan na Afrilu amma shuru kake ji tamkar an aiki bawa garinsu.

Sai dai Malam Bolaji Abdullahi ya shada min cewa an riƙa ɗage taron ne "saboda wasu dalilai na tsare-tsare."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu ( na dama) ya taka muhimmiyar rawa wajen yin nasarar APC

"Tun da muka kafa jam'iyyar nan muka amince cewa ba za mu riƙa yin amfani da kuɗin gwamnati wajen gudanar da ita ba; sai dai mu riƙa samun gudunmawa daga 'yan jam'iyya shi ya sa ake samun matsala wurin kiran taron. Na biyu kuma akwai matuƙar wahala bakin kowanne ɗan jam'iyya ya zo ɗaya a kan lokacin da za a gudanar da taron. Don haka wanna ba batu ne na samun matsala a jam'iyya ba," in ji Mallam Bolaji Abdullahi.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin rashin gudanar da babban taron jam'iyyar na da alaka da barakar da ke tsakanin wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Dr Kari ya ce, "Rashin gudanar da tarukan jam'iyya ya sa ana samun rauni a cikinta; kuma saboda halin ko in kula da ake nuna wa jam'iyyar shi ya sa ba a tuntubarta a al'amuran da suka shafi gudanar da gwamnati, hakan ne ma ya sa kake ganin dukkan naɗe-naɗen da shugaban ƙasa ke yi wasu 'yan tsiraru ne ke yi, ba a la'akari da irin rawar da wasu suka taka wajen cin zaben wannan gwamnatin."

Sai dai fadar shugaban ta sha musanta cewa ba ya tuntuɓar jam'iyyar, suna masu cewa babu wata matsala tsakaninsa da shugabannin jam'iyyar.

A cewarsa, matakin farko da APC za ta ɗauka domin shawo kan matsalolin da ke addabarta shi ne: ta dauki kwararan matakai na hadan kan 'ya'yanta da kuma sakin mara ga ɓangarorin jam'iyyar irinsu kwamitin amintattu, babban kwamitin zartarwa na kasa, kwamitin gudanarwa da kuma rassanta na jihohi.

Masanin kimiyyar siyasar ya ƙara da cewa dole Shugaba Buhari ya fahimci akwai buƙatar ya tsaya tsayin daka wajen ci gaban jam'iyyar, ko da ba zai sake yin takara ba "domin kuwa ko ba komai ita ce dokin da ya hau ya zama shugaban ƙasa, bai kamata ya sa ido ya ga darewarta ba."

'Yan ƙasar da dama za su zuba ido su ga yadda al'amuran jam'iyyar za su ci gaba da gudana musamman a lokutan da zabukan shekara ta 2019 ke ƙara ƙaratowa.

Labarai masu alaka