Su wane ne suka yi yunƙurin kashe Dino Melaye?

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an 'yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi holin wasu mutane da makaman da aka samu a wurinsu, wadanda ta zarga da yunkurin kashe wani dan majalisar dattijan kasar, Sanata Dino Melaye a watan Afrilu.

Cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Jimoh O. Moshood ya fitar, rundunar 'yan sandan ta ce daga cikin mutanen da ake zargi, akwai wasu manyan 'yan siyasa a jihar Kogi, wadanda ta ce su ne suka shirya harin.

Rundunar 'yan sandan ta ce bincike ya nuna wani babban dan siyasa ne ya bai wa wani da a ka fi sani da "Iron" ko karfe, izinin kai wa Sanata Dino Melaye hari.

"Daga nan ne "Iron" ya dauki hayar wasu mutane da suka kware wajen kisa domin aiwatar da nufinsu," Inji sanarwar.

Har yanzu dai ba a kama "Iron" din ba, amma sauran mutanen da ya dauka hayar sun shiga hannun hukuma.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Senate
Image caption Sanata Dino Melaye

Acewar sanarwar, makaman da a ka samu a wajen mutanen sun hada da bindigogin AK 47 guda biyar, da pistol daya, da bindigogi kirar gida biyu da harsasai masu yawa.

Rundunar 'yan sandan ta ce daya daga cikin mutanen ne ya kai rahoto don kashin kan shi ga 'yan sanda bayan sun yi yunkurin halaka dan majalisar.

Rundunar ta ce ta zafafa bincike domin kamo sauran mutanen da ke da hannu a cikin harin, sannan za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Har yanzu dai mutanen da ake zargi ba su ce komai ba game da zarge-zargen da a ke musu.

A tsakiyar watan Afrilu ne wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan Sanata Dino Melaye a Aiyetoro-Gbede a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, lokacin da yake cikin gidan da dare.

'Yan bindigar ba su samu kai wa gare shi ba, amma sun lalata katangar gidan da harsasai.