Wata uwar 'boge' ta mayar da 'yar da ta saya

Surrogate baby Hakkin mallakar hoto CHRISTOPHER FURLONG/GETTY IMAGES
Image caption An ba wa wani gidan marayu jaririyar (ba ita ce a wannan hoto ba) don samun kulawa

An zargi wata mace 'yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mai da jaririyar da ta saya, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar 'yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800, kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jaririyar ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Ba da goyon ciki a ƙasar Italiya, haramtaccen abu ne kuma akan ɗaure mutum a gidan yari a ci shi tara mai tsanani.

An ce uwar 'bogen' ta faɗa wa 'yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.

Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu.

'Jaririyar ruwa biyu ce'

Mahaifiyar jaririyar, 'yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali.

Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar.

Don haka, bayan kwana uku, rahotanni sun ce, sai ta mayar da jaririyar.

An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista.

Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami'ai suka sake tuntuɓa - sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana.

Hakan ya sanya fargaba lallai da walakin, don haka sai suka ankarar da 'yan sanda.

Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome.

A yanzu dai ba ta fi tsawon wata guda a duniya ba, kuma an damƙa ta gidan marayu don kula da ita.

An zargi wata mace 'yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mayar da jaririyar da ta sayo, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar 'yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800 kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jarirai ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Al'adar ba da goyon ciki haramun ne a ƙasar Italiya, inda akan yi mutum ɗauri a gidan yari da cin tara mai tsanani.

An ce uwar bogen ta faɗa wa 'yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.