Joshua ya tamfatse Klitscko a zagaye na 11

Joshua and Klischko Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bugun da Joshua ɗan asalin Nijeriya ya yi wa Klischko ya sanya tsohon zakaran boksin ɗin ganin faɗuwarsa ta biyar

Anthony Joshua ya yi wani gagarumin ƙwazo ta hanyar ƙara wa kambunsa, lambar zakaran boksin ajin masu nauyi ta duniya saboda bajintar buge Wladimir Klitschko a filin wasa na Wembley.

'Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar tsallen-baɗake, inda Joshua ɗan boksin ɗin Burtaniya, ya buge tsohon gwarzon duniyan a zagaye na biyar, kafin a kai shi ƙasa a zagaye na shida - karon farko a fafatawa 19 da ya yi.

Duka 'yan damben boksin ɗin sun fuskanci shan kaye a wannan karawa da za ta daɗe a zukatan mutane, kafin Joshua ya yi wa abokin karonsa dukan zauna-ka-ci-doya a zagaye na 11.

Joshua, wanda iyayensa 'yan Nijeriya ne, ya sauke wa Klitschko wani wawan naushi da ya ba shi damar kai shi ƙasa cikin laulayi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Klitschko aka fara kai wa ƙasa a zagaye na biyar
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai dai irin wannan ƙaddara ta faɗa wa Joshua a zagaye na shida

Klitschko ya yi ta maza ya sake jan zare, bayan an sa shi a maƙatar hagu daga bisani.

Sai da lafari David Fields ya karɓe shi lokaci da aka takure shi a jikin igiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau biyu ana kai Klischko ƙasa a zagaye na 11 kafin lafari ya karɓe shi

Joshua ya cira hannuwansa sama lokacin da ihu da sowa suka ɓarke a filin Wembley.

Ya tsallake karawarsa mafi zafi a yau, yayin da Klitschko ya gane irin wayon da yake da shi.

Ko da yake, ya nuna har yanzu duk da shekarunsa 41, za a ci gaba da kai ruwa-rana da shi a fagen karawa ta duniya.

Klitschko zai ciji yatsa a kan rashin gama wa Joshua aiki, lokacin da ya shimfiɗe shi ƙasa, har ma aka riƙa ganin ba wata makawa ya kusa sake karɓar biyu daga cikin kambun da ya rasa a hannun Tyson Fury a shekara ta 2015.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ingila Rio Ferdinand na daga cikin mutanen da suka taya Joshua murna

"Me zan ce? Karawa 19, ba a buge ni ba, a shekara uku da rabi," in ji Joshua. "Ban cika bakin na fi kowa ba, amma dai ludayina ne ke kan dawo. Ka san kuma ba a ƙwace wa yaro garma.

"Kamar yadda 'yan boksin ke cewa, ajiye girman kanka a waje kuma ka mutunta abokin karawarka. Don haka ina yi wa Wladimir Klitschko jinjinar ban girma."

Labarai masu alaka