Bayan ƙara kyau, ko dashen mama na da wata illa?

Plastic surgery Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akan yi amfani da roba ko balan-balan ɗin silicon don mayar da tsohuwa yarinya

Dashen mama, nau'in kwalliyar mata ce ta cikin jiki da ya fara samun wajen zama a ƙasashe kamar Nijeriya, don kuwa su ma ba sa so a ga tsufansu.

Mata kan yi wannan kwalliya ce ta yadda za a riƙa ganinsu gwaɗas da ƙuruciya, bayan ƙara burgewa da jan hankali.

Tun tale-tale, mata sun shahara wajen son gyaran jiki, a cancanɗa gayu don kyaun gani da kuma fita kunya.

A baya Turawa aka sani da kwalliyar dashen mama, kafin yanzu da take ƙara bazuwa a duniya.

Matan Nijeriya, 'yan ƙwalisa ne masu son su jera da zamani, ga kuma son tsere sa'a, kuma ba sa son a ga tsufansu.

Shin yaya ake dashen mama?

Wani ƙwararren likitan fida, Dr. Sa'ad Idris ya ce fiɗa ake yi nono, a tsarga shi don yi masa ƙari ko ciko.

Ana amfani da wani abu mai kama da balan-balan, inda ake sanya ta daidai da surar maman.

Shi wannan abin mai kama da balan-balan ana kiransa Silicon da kuma wani sinadari mai alaƙa da gishiri da ake zuba shi a cikin balan-balan ɗin silicon.

Akan yanka ƙoramu ko jijiyoyin da suka haɗa kan nono da sauran gangar jiki.

Ko mai dashen mama na iya shayarwa?

Dr. Sa'ad Idris ya ce binciken da aka yi, ya nuna cewa likitoci ba su cika ba wa wadda ta yi dashen mama shawarar ta shayar da jariri ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata kan kashe maƙudan kuɗi don ganin sun yi wannan kwalliya ta burgewa

"Yanka ƙoramun nono da aka yi, kan sa ruwan nono zai janye."

Haka zalika, sinadaran da aka zuba a cikin balan-balan ɗin silicon a wasu lokuta ka iya tsiyaya, kuma idan jariri ya sha, suna iya illata shi.

Ko dashen mama na da wata illa?

Dr. Sa'ad Idris ya ce dashen mama kamar kowacce irin tiyata, ta jiɓanci yanka jikin mutum da kuma ba da maganin kashe kaifi.

A cewar likita hakan na da matsaloli, don kuwa wasu idan suka kwanta, ba lallai ne su sake tashi ba, idan an gamu da matsala.

Haka kuma "akan iya samun jini ya tattaru a wurin da aka yanka, ballantana inda aka sanya balan-balan ɗin silicon."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu irin wannan dashen mama ya bazu a duniya

Ko yaushe mace za tai ta jin ciwo ga mamanta bayan an yi dashe.

"Maimakon ma a gyara...(ƙirjin mace ya zama cas a tsaye) ƙila ɗaya ya fashe," in ji likita.

A cewarsa (fatar) nonon ka iya canza launi, ko kuma girmansa ya ragu.

Sai dai a iya sanina da kuma binciken da muka yi, "ban ga inda aka alaƙanta dashen mama da cutar sankara ba, in Dr. Sa'ad Idris."