Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa - David Mark

Mr Mark [daga dama] ya ce ya yi mamakin yadda Jonathan ya kasa gane makircin da ake shiryawa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Mark [daga dama] ya ce ya yi mamakin yadda Jonathan ya kasa gane makircin da ake shiryawa

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark ya ce ya gargadi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan irin makircin da 'yan arewacin kasar ke shiryawa domin kayar da shi a zaben 2015.

Mr Mark, wanda ya bayyana hakan a littafin Against the Run of Play, wanda fitaccen mai sharhin nan na jaridar ThisDay Olusegun Adeniyi ya wallafa, ya ce da gangan jam'iyyar PDP, a karkashin Ahmad Adamu Mu'azu ta gaya wa Mr Jonathan cewa zai lashe zaben bisa dogaro da hasashe kan tsarin kada kuri'ar da 'yan arewacin kasar za su yi.

A cewarsa, "Na tsinkayi faɗuwar sa [Jonathan] zaben kuma na nuna masa hakan, sannan na bayyana masa cewa hasashen da wasu mutane da ke kusa da shi suka yi kan tsarin kada kuri'ar da za a yi a Arewa ba daidai ba ne."

"Na gane makircin da aka kitsa da kuma taron dangin da aka yi a Arewa domin ganin Jonathan bai cimma burinsa ba amma ba sarkin yawan ya fi sarkin karfi, domin wadanda ke kusa da shi na ganin babu yadda shugaban kasa da ke kan mulki, kuma a jam'iyyar PDP ya fadi a zabe," in ji Mr Mark.

Tsohon shugaban majalisar ta dattawan Najeriya ya ce wasu mutane sun rika yaudarar Mr Jonathan suna gaya masa cewa ba zai sha kaye a zabe ba kuma mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo ya gane cewa yaudarar tsohon shugaban kasar ake yi "amma ban san irin tasirin da yake da shi a yakin neman zaben ba. Kuma har yanzu ian matukar mamakin yadda Jonathan ya kasa gane cewa ana yaudararsa har sai da lokaci ya kure".

Mr Mark ya ce Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka sa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal bijire musu saboda wulakacin da suka rika yi masa.

A cewarsa, sun yi zaton shi da Tambuwal na son yin takarar shugabancin kasar a shekarar 2015, amma "na gaya wa Jonathan ni da shi cewa duk wadanda ke ba shi irin wadannan labaran karya suke yi."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau hudu Mr Mark ya zama dan majalisar dattawa

Zan faɗi gaskiya abin da ya faru

Shi dai tsohon shugaban na Najeriya ya ce tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ne suka sa ya sha kaye a zaben 2015.

Mawallafin littafin ya ambato Mr Jonathan na cewa Shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama da jami'an gwamnatinsa sun bayyana masa ƙarara cewa suna son sauyin gwamnati a Najeriya kuma za su iya yin komai domin cimma hakan.

A cikin gida kuma, tsohon shugaban ya ce shugaban hukumar zabe na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya yi masa abin da bai yi tsammani ba, saboda har yanzu nan ya kasa fahimtar abin da ya sa Jegan ya nace cewar ya shirya wa yin zabe lokacin da kashi 40% bisa dari na masu zabe ba su karbi katinsu na zabe ba.

Ya ce ya gana da shugaban hukumar zabe ya bayyana masa damuwarsa kan yi zaben a watan Fabrairun 2015, amma ya kafe cewar ya shirya wa zaben domin Amurkawa sun ingiza shi abin da ba za taba yi a kasarsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Goodluck Jonathan ne shugaba mai ci na farko da ya fadi zabe a Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya musanta wannan zargi, yana mai cewa zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari zabi ne da nuna abin da 'yan Najeriya ke so.

Shi ma tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya ya musanta hakan, inda ya ce na'urar tantance zaben da aka yi amfani da ita a 2015 ta hana kowanne irin magudi.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya ce zai buga littafin da zai fayyace gaskiyar abin da ya sanya shi faduwa zaben shekarar 2015.

Labarai masu alaka