Harin Madina: Saudiya ta kama mutane 46

Saudi Arabia
Image caption A karshen azumin watan Ramadanan bara ne aka kai harin a Madina

Saudiya ta ce ta kama mutane arba'in da shida, bayan harin kunar bakin wake da a ka kai a birnin Madina bara.

Akasarin mutanen 'yan kasar ta Saudiya ne, amma an ce akwai goma sha hudu 'yan wasu kasashe da suma a ke tsare da su.

Saudiya ta ce mutanen, mambobin wata kungiyar 'yan bindiga ce da ta kai harin, a inda a ka kashe jami'an tsaro hudu.

A lokacin da a ka kai harin, an dora alhakin shi ne a kan kungiyar IS.

Harin ya auku ne a watan Yulin bara, a karshen azumin watan Ramadana.

Ba dai a san lokacin da a ka yi kamen mutanen ba.