'Dalilin da ya sa muka kama Sule Lamido'

Wasu dai na ganin bakin tsohon gwamnan ba ya mutuwa
Image caption Sule Lamido ya yi gwamna karo biyu a jihar Jigawa

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido bisa kalaman tunzura al'umma.

DSP, Sambo Sakkwato wanda shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan shiyya ta daya da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa sun samu korafi ne daga gwamnatin jihar Jigawa kan kalaman tunzura jama'a.

Ya ce babban laifi ne furta kalaman da za su iya tayar da hankali ko kuma hatsaniya, babban laifi ne.

DSP Sambo ya ce duk da cewa rundunar ta gayyaci tsohon gwamnan ne amma ba za ta iya tabbatar da hakikanin lokacin da za a sake shi ba.

An dai kama Sule Lamido ne a gidansa da ke Sharada a Kano da safiyar ranar Lahadi.

Sule Lamido dai ya bukaci magoya bayansa na jam'iyyar PDP a jihar Jigawa da su kare kuri'unsu a zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

Wani makusancin Sule Lamidon, Alhaji Ndagi Malanmadori ya shaida wa BBC cewa " Sule Lamido ya nanata abin da shugaba Buhari yake fada ne cewa 'A kasa, a tsare sannan a raka' saboda haka ni ban ga laifin mai gida ba."

Alhaji Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma a 'yan kwanakin nan, ya yi ta sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC.