Nigeria: PDP ta yi Allah-wadai da kama Sule Lamido

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Jam'iyyar adawa ta PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya

A Najeriya babbar Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi Allah-wadai da kama daya daga cikin jagororinta, Alhaji Sule Lamido, wanda 'yan sanda suka yi.

A wata sanarwar da kakakin jam'iyyar Dayo Adeyeye ya fitar ranar Litinin, jam'iyyar ta ce dalilin da 'yan sanda suka bayar na kama shi ba shi da tushe balle makama, tana mai karawa da cewar an kama tsohon Gwamnan ne saboda zaben kananan hukumomin da za a gudanar a jiharsa ta Jigawa.

A ranar Lahadi ne dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta Najeriya ta kama Sule Lamido kan zargin tunzura jama'a.

Jam'iyyar ta ce maganar zaben kananan hukumomin ne ta sa aka kama tsohon gwamnan Jigawan da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam.

PDP ta yi kira ga jami'an tsaro su saki Alhaji Sule Lamido da Gabriel Suswam da kuma tsohon gwamnan jihar Neja, Mu'azu Babangida Aliyu.

Ana tsammanin 'yan sandan kasar za su gurfanar da Sule Lamido gaban kotu bayan sun gama bincike.

Labarai masu alaka