A India an kashe Musulmi biyu bisa zargin satar saniya

Indiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu addini Hindus na ganin sharu tsarkarkiya

'Yan sanda a Indiya sun ce an kashe wasu Musulmai biyu da aka yi zargin suna kokarin sace wasu shanu.

Irin wadannan kashe-kashe a arewa maso gabashin jihar Assam na cikin jerin hare-haren da ke haifar da tashin hankalin addini saboda irin kimar da ake dukar shanu da ita.

Mabiya addinin Hindu na ganin shanu a matsayin halittu masu tsarki don haka kashe su keta doka ne a jihohi da dama.

Wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta fitar a makon da ya gabata na nuna cewa akalla Musulmai 10 aka kashe ta irin wannan hanya tun watan Mayun 2015.

'Yan sanda sun ce wadanda aka kashe a ranar Lahadi a gundumar Assam's Nagaon sunayensu Abu Hanifa da Riyazuddin Ali.

Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito babban jami'in 'yan sanda Debaraj Upadhyay na cewa "'Yan kauyen sun runtuma a kansu, suka yi musu dukan tsiya da sanduna saboda zargin suna kokarin sace shanu.

"Kafin mu kai su asibiti da dare sun mutu sakamakon raunukan da suka yi."

'Yan sanda sun ce an tsare mutum biyu domin yi musu tambayoyi.

Human Rights Watch ta ce tun lokacin da jam'iyyar Bharatiya Janata ta mabiya Hindu ta hau karagar mulki a shekara 2014 a Indiya, hare-haren da ake kaiwa kan Musulmai da mabiya addinin Dalit sun karu saboda zarginsu da akan yi da saya ko sayar da ko kashe shanu.

Wadanda aka kashe a tashe-tashen hankula domin yaki da amfani da naman shanu a Indiya sun hada da wani yaro mai shekara 12.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar kare sharu na lura da motoci a jihohi daban-daban

Jihoji da dama sun kaddamar da doka dake hana kashe shanu.

A watan Maris a yammacin jihar Gujarat an yi wata doka wadda ta tanadi hukuncin daurin rai-da-rai a kan duk wanda ya kashe saniya.

Labarai masu alaka