Mutum 27 sun ji rauni sakamakon girgiza a jirgin saman Aeroflot

jirgin saman Aeroflot Hakkin mallakar hoto RR / Reuters
Image caption Mutane da dama sun ji rauni da jirgin saman Aeroflot ya gargaza

Akalla mutum 27 ne suka ji rauni a sakamakon girgizar da wani jirgin sama na kamfanin Aeroflot, da suke ciki ya yi, wanda ya taso daga babban birnin Rasha, Moscow, birnin Bangkok na Thailand.

Jami'an Rasha sun ce babu wani da ya ji raunin da zai iya kaiwa ga salwantar rai amma fasinjoji da dama sun karye inda guda uku ke bukatar tiyata.

Wani fasinja ya bayyana cewa ya ji an yi jifa da shi sama lokacin da yake kokarin rike wani abu don kada ya fadi.

Kamfanin jirgin saman ya ce girgizar ta faru ne a sararin sama don haka masu aikin jirgin ba za su iya ankarar da fasinjojin game da matsalar ba.

A wata sanarwa da kamfanin na Aeroflot ta fitar ya ce dalilin da ya sa wasu suka ji rauni shi ne wasu fasinjojin ba su sa madaurin fasinja na kujera ba.

Hotuna da aka bayyana na nuna wadanda suka ji rauni, kwance tsakanin kujerun jirgin da abinci da sauran abubuwa warwatse.

Wata fasinja mai suna Yevgenia ta bayyana wa kamfanin watsa labarai na Rossiya 24 ta hanyar waya cewa ''Girgizar ta jefa mu sama kuma, ba ta yadda za mu iya rike wani abu.''

Sai dai ofishin jakadancin Rasha a Thailand ya ce 'yan Rasha 24 ne suka ji rauni yayin da kuma wasu 'yan Thailand guda uku.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Interfax cewa mutum 15 da yaro daya aka kai asibitoci a Bangkok

Kamfanin jirgin saman ya ce mutane 313 ke cikin jirgin mai lamba SU 270.

Labarai masu alaka

Karin bayani