Nigeria: Sule Lamido zai gurfana a gaban kotu

Wasu dai na ganin bakin tsohon gwamnan ba ya mutuwa
Image caption Sule Lamido ya yi gwamna karo biyu a jihar Jigawa

Wata majiya a rundunar 'yan sanda ta shiyya ta daya da ke Kano ta shaida wa BBC cewa za ta gurfanar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban kotu, ranar Talata.

Majiyar ta ce Sule Lamido zai bayyana ne a gaban kuliya a tsohuwar jihar da ya mulka wato Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa ce dai ta kai koken cewa tsohon gwamnan ya yi kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina.

A ranar Lahadi ne dai 'yan sanda suka kai samame gidan Sule Lamido da ke a birnin Kano.

Kuma a ranar ne suka gayyace shi domin bayani kan laifin da ake tuhumar sa da shi.

An dai ce Sule Lamido ya fada wa taron magoya baya cewa, "su kasa, su tsare sannan su kuma raka akwatinan zabensu," a zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihar.

Wasu magoya bayan Sule Lamido dai na kallon kama tsohon gwamnan kamar yunkurin toshe bakin masu hamayya ne.

Sun bayyana cewa a baya ma shugaba Buhari ya sha amfani da irin wadannan kalamai a tarukan kamfe na neman zabensa.