Ya kamata 'Buhari ya bi shawarar likitoci ya tafi hutun jinya'

Buhari Hakkin mallakar hoto Kaduna state government
Image caption Buhari ya ce bai taba yin jinya irin wacce ya yi a London ba

Wasu daga manyan kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki hutu domin yin jinyar rashin lafiyar da ke damunsa.

Rashin bayyanar shugaban a taron majalisar zartarwa sau biyu a jere da kuma kasa halartar sallar Juma'a, ta sa ana ta ce-ce-ku-ce a kan halin lafiyarsa.

A sanarwar da suka fitar, masu fafutikar, da suka hada da lauya Femi Falana da Farfesa Jibrin Ibrahim da Auwal Rafsanjani, sun ce:

"Ya zama wajibi a garemu mu ba shi shawara ya bi umarnin da likitocinsa suka ba shi ta hanyar daukar hutu domin ya kula da lafiyarsa."

Kusan mako biyu kenan rabon da a ga Shugaba Buhari a bainar jama'a, abin da ya sa 'yan kasar ke tambayar ko ina shugaban ya ke, ta hanyar amfani da maudu'in #WhereIsBuhari a shafin Twitter.

Wannan kuma ya sa fargaba a zukatan wasu 'yan kasar musamman magoya bayansa, inda wasu rahotanni ke nuna cewa rashin lafiyar tasa ta kara ta'azzara.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al'amura.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati

'Yan kungiyoyin farar hular, wadanda ke da kima a idanun jama'a a ciki da wajen Najeriya, sun kuma yi amfani da wani shashi na jawabin da mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ya yi, inda ya ce likitocin shugaban sun bashi shawarar ya rinka bi a hankali kafin ya gama murmurewa.

A watan Maris ne ya dawo daga hutun jinya na mako bakwai a Birtaniya, sai dai bai bayyana ainahin cutar da ke damunsa ba.

A ranar Laraba ne hukumomi suka ce shugaban zai yi aiki daga gida, inda za a rika kai masa fayil-fayil da sauran muhimman abubuwan da ke bukatar sanya hannunsa bayan da ya gaza halartar taron majalisar zartarwa.

'Yan kasar da dama na ganin shugaban bai halarci taron ba ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wasu na nuna damuwa kan halin da yake ciki.

Kawo yanzu babu wani martani a hukumance daga gwamnati kan kiran da 'yan farar hular suka yi.

Labarai masu alaka