Nigeria: Kotu ta tura Sule Lamido zaman waƙafi

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido
Image caption Jami'iyyar PDP ta Sule Lamido ta ce kamen nasa siyasa ce kawai, abin da APC ta musanta

Wata kotun majistare da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta tura tsohon gwmanan jihar Sule Lamido zuwa gidan kaso, har sai ranar 4 ga watan Mayun sekarar 2017 inda za a ci gaba da sauraron karar.

A ranar Talata ne aka gurfanar da Sule Lamido a gaban kotun bayan da gwamnatin jihar ta kai kararsa bisa zargin yin kalaman tunzura jama'a.

An tuhume shi da aikata laifuka hudu da suka danganci neman tayar da zaune tsaye, amma tsohon gwamnan ya yi watsi da zargin.

Lauyoyinsa sun bukaci a bayar da belinsa, sai dai lauyoyin gwamnati sun ki yarda da hakan, inda suka nuna wa alkalin cewa laifukan da ake tuhumarsa a kansu sun yi girman da bai kamata a bayar da belinsa ba.

Daga bisani alkalin ya ki amincewa da bayar da belin Sule Lamidon har sai an sake zaman kotun a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, inda kafin sannan zai kasance a gidan kaso.

Bayan hukuncin hana belin nasa an samu yamutsi a harabar kotun, inda magoya bayan tsohon gwamnan suka fara zanga-zanga.

Sai da jami'an tsaro suka dinga harba hayaki mai sa hawaye sannan suka iya tarwatsa masu zanga-zangar.

Tun da fari dai Sule Lamido ya bayyana cikin kayansa na gida kuma yana murmushi tare da daga hannu ga magoya bayansa, wadanda suka yi cincurundo a kusa da kotun.

A ranar Lahadi ne 'yan sanda suka kama tsohon gwamnan a birnin Kano bayan gwamnatin jihar ta zarge shi da yin kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina.

Sai dai magoya bayansa sun ce jagaoran nasu kawai ya cewa jama'a ne, "su kasa, su tsare sannan su kuma raka akwatinan zabensu" a zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihar.

Image caption An tsaurara tsaro a ciki da wajen kotun

Wakilin BBC Ibrahim Isa, wanda ya halarci zaman kotun, ya ce daruruwan magoya bayan tsohon gwamnan manya da kanana ne suka hallara a kotun dauke da fastocin jam'iyyarsa ta PDP.

Ya kara da cewa an tsaurara tsaro, inda 'yan sanda suka kewaye kotun daga nisan kimanin mita 200.

Shi dai Sule Lamido, wanda ya mulki jihar daga shekarar 2007 zuwa 2015, ya yi fice wurin sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

Jam'iyyar PDP ta ce kamen nasa wani yunkuri ne na dakile kaifin 'yan adawa a kasar, sai dai gwamnatin APC ta musanta hakan.

Babu shakka wannan shari'a za ta dauki hankalin masu lura da al'amura da ma sauran 'yan kasar, ganin zargin da wasu ke yi cewa tana da alaka da siyasa.

A baya dai Shugaba Buhari ya sha amfani da irin wadannan kalamai da magoya bayan Lamido suka ce su kawai ya yi, a tarukan kamfe na neman zabensa.

Labarai masu alaka