'Ana zargin Buhari da ɓoye halin lafiyarsa'

Nigeria"s President Muhammadu Buhari signs the instrument of ratification of the Paris Agreement on climate change in Abuja, Nigeria March 28, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhamadu Buhari ya koma bakin aiki ne a watan Maris bayan ya yi jinya a Birtaniya

A jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, babban editan jaridar Daily Trust ta Najeriya, Mannir Dan Ali, ya rubuto cewar an zargi Shugaba Muhammadu Buhari da ɓoye yanayin lafiyarsa kamar yadda takwaransa na Amurka, Donald Trump, ya ɓoye adadin harajinsa.

'Yan Najeriya suna kara damuwa game da lafiyar Shugaba Buhari, suna masu fatan shugaban ba zai mutu kan karagar mulki ba, kamar yadda Shugaba Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu a shekarar 2010 bayan doguwar rashin lafiya wadda ta sa ya je neman magani a Jamus da Saudiyya.

Rashin halartar Buhari zaman majalisar ministoci biyu a jere da kuma rashin zuwa masallacin Juma'ar da ke da nisan minti daya daga ofishi da gidansa sun ruruta damuwar a baya-bayan nan.

Gwamnatin kasar ta fitar da bayanai kadan game da lafiyarsa, kuma babban jami'in tsaron shugaban kasa ya kori wani dan jarida da ke aiki a daya daga cikin manyan jaridun kasar bayan ya rubuta labari kan damuwar ta baya-bayan nan.

Masu taimaka wa Buhari kan watsa labarai sun nisanta kansu daga matakin da jami'in ya dauka, kuma sun sa wani babban jami'i ya soke korar da aka yi wa dan jaridar.


Mannir Dan Ali:

Hakkin mallakar hoto Mannir Dan Ali

"Shugaban ya rage ayyukansa a hukumace kuma ya daina fita daga fadar shugaban kasa"


Lamarin ya nuna cewar masu taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai ba sa jin dadin tunkarar su da ake da tambayoyi game da lafiyar tsohon shugaban mulkin sojan. Amman basu yi sa'a ba domin babu alamar cewar batun ya kusa kaucewa.

Bayan ya dawo daga jinyar mako bakwai a Birtaniya a farkon watan Maris, Buhari ya ce bai taba irin wannan rashin lafiyar ba, kuma ya ce an kara masa jini ba tare da cikakken bayanin yadda aka yi ba.

Sahihan rahotanni sun ce likitocinsa na Birtaniya sun je Najeriya domin su kula da shi, amma ba a tabbatar da rahotanin ba.

Shugaban ya rage ayyukansa a hukumance kuma ya daina fita daga fadar shugaban kasa.


Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Janairu: Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"

5 ga watan Fabrairu: ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris: Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu: Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"

28 ga watan Afrilu: Bai halarci Sallar Juma'a ba


A da, yana halartar zaman majalisar ministoci na mako-mako da kuma sallar Juma'a inda abokansa ke samu su gaisa da shi.

Amman bayan ya kasa halartar zaman majalisar ministoci na ranar Laraba, ministan yada labari, Lai Mohammed, ya shaida wa manema labarai cewar bisa shawarar likitocinsa, Buhari zai yi aiki daga gida a ranar, kuma ya nemi a kai masa fayel-fayel din da ke bukatar ya yi aiki a kansu gida.

A dai-dai lokacin da da yawa daga cikin 'yan Najeriya ke bin kiran da ministan ya yi na yin addu'ar Allah ya bai wa Shugaban lafiya ba da jimawa ba, wasu, kaman marubucin nan da ya ci kyautar Nobel, Wole Soyinka, suna cewa ya kamata shugaban ya bayar da cikakken bayani kan lafiyarsa.

A wata sanarwa, Soyinka ya ce: "Boye yanayin lafiyarka kamar yadda Donald Trump yake boye adadin kudin harajinsa ba abu ne da muke tsammani daga wani shugaban Najeriya ba."

Babu tabbacin ko Buhari zai yi karin haske game da lafiyarsa, amman mutane suna fatan cewar shugaban, wanda ya kai rabin wa'adin mulkkinsa, zai samu sauki nan ba da jimawa ba soboda ya mayar da hankali kan dakile kalubalen da ke fuskantar Najeriya, ciki har da karayar tattalin arziki mafi girma tun karshen mulkin soja a shekara 1999.

Labarai masu alaka