Ina shugaban Nigeria Buhari yake?

Buhari Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Wasu 'Yan Najeriya suna son a bayyana musu halin da Shugaba Buhari yake ciki

Rahotanni da ke fitowa daga fadar shugaban Najeriya na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fito ofishinsa na cikin gida ya yi aiki har ma ya gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

Abokin aikinmu Haruna Tangaza ya ziyarci fadar shugaban kasar a ranar Talata inda ya ce ya zagaya ko ina a harabar ofis din shugaban da na matiamakinsa, "Na ga jami'an tsaro a ofis dinsa, an kuma shaida min cewa ya fito ofis har ya gana da mutum biyu da ministan shari'a da shugaban kamfanin mai na kasa NNPC."

Haruna ya kuma ce yana tsaye ya ga fitowar jami'an har ma ya zanta da su.

Ya zanta da shugaban kamfanin NNPC Mai Kantu Baru, inda ya shaida masa yadda ganawarsa ta kasance da shugaba Buharin.

"Yanzu na fito kuma kamar yadda ku ka ga ni tun 11.30 na safe na shiga har karfe biyu na rana, mun tattauna na tsawon fiye da sa'a daya, kuma ba a kwance na ganshi ba," in ji Mista Baru.

Ya kara da cewa, "Na masa bayani ya kuma fahimta. Ba zai yiwu mu yi hirar sa'a daya ba in har ba shi da lafiya."

Na zanta da mai magana da yawun shugaban - Haruna Tangaza

A zantawar da na yi da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, ya shaida min cewa a garesu wannan kiraye-kirayen da kungiyoyin fararen hula ke yi ne cewqa shugaban ya koma asibiti duk kokarin ne na karkarta da hankalin shugaban kan kokarin da yake na yaki da cin hanci da rashawa wanda ya yi zafi a yanzu.

Malam Garba Shehu ya ce kiraye-kirayen na 'yan siayaysa ne da ke son wargaza yaki da cin hanci da rashawa ko kuma suna so a dama da su a gwamnatin amma an ki.

Ko Buhari na shiga ofis dinsa?

Haruna ya ce ba a babban ofis din shugaban da ke fadar gwamnati shugaba Buharin ya yi aiki ba.

"Ya yi aikin ne daga ofis dinsa na cikin gida da aka tsara masa musamman don ya dinga aiki daga can, amma cikin babban ofishin da ke fadar shugaban kasa a ke shiga."

Kwanan nan zan koma asibiti — Buhari

Labarai masu alaka