Somalia: Yara miliyan daya na fama da tamowa

Iyaye mata 'yan somaliya Hakkin mallakar hoto Unicef/Mackenzie Knowles-Coursin
Image caption Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya yayi kiyasin yara fiye da miliyan guda ne ke fama da tamowa a somaliya.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya yi kiyasin cewa yawan yaran da ke somaliya, wadanda ke fama da ma kuma wadanda za su yi fama da tamowa ya karu da kaso 50 cikin 100 tun farkon wannan shekarar.

Alkaluman da Asusun ya yi kiyasi ya nuna cewa yara miliyan 1.4 ne ke fama da tamowa.

A cikin wadannan alkaluman, UNICEF ya ce yara sama da 250 za su yi fama da tamowar da za ta yi barazana ga rayuwarsu.

Ya kara da cewa hakan zai iya jawo cututtka irin su amai da gudawa da kuma kyanda.

Somaliya na fuskantar fari mafi muni a cikin shekara 10.

UNICEF ya ce an fara ruwan sama da ake yi a shekara a tsakanin Afrilu da Yuni, kuma hakan yasa ana samun saukin farin a wasu sassa na kasar.

Labarai masu alaka