An kama wani ango saboda gayyatar baƙin bogi a bikinsa

Sin Hakkin mallakar hoto Shaanxi TV
Image caption Ango ya biya mutane domin su halarci aurensa

An kama wani mutum a arewacin kasar Sin a ranar bikin aurensa bayan da 'yan uwan matarsa suka gano cewa ya biya baki 200 domin tsaya a matsayin iyalinsa da abokansa.

Bayani daga kafofin watsa labarai a lardin Shaanxi na nuna cewa 'yan uwan matar Liu, sun fara zaton haka ne a lokacin da suke hira da wasu daga bangaren angon, wadanda suka ce su abokanansa ne kawai, amma basu iya nuna yadda suka san juna ba.

A lokacin da aka fara bikin auren, ba alamar iyayen angon, sai komai ya bayyana.

A wata hira da tashar talibijin a yankin Shaanxi TV ta yi da bakin, sun ce angon mai suna Mista Wang ya biya su dala 12 a rana domin su tsaya a matsayin 'yan uwa da abokansa.

Wasu suka ce su dirabobi ne, wasu kuma dalibai ne, inda daya daga cikinsu ya nuna hirar da ya yi da angon a kan dandalin WeChart, da suke tattaunawa a kan farashin da zai biya domin ya zo bikin.

Sai dai a bangaren amarya, rahotannin na nuna cewa ma'auratan na tare shekara uku kenan, amma bata lura da wani abu ba saboda suna da abokai daban-daban.

Har yanzu ba a gano dalilin da yasa angon ya yi hakan ba ko kuwa wata doka da ya karya.

Wasu kafofin watsa labarai sun ce 'yan uwan matar ba su yarda da auren ba saboda angon ba shi da kudi, don haka ya hana 'yan uwansa zuwa bikin.

Sun kuma kara da cewa 'yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin.

Da yake mutane da dama na kokarin sanin sakamakon bikin auren, masu amfani da shafukan sada zumunta na kokarin gano abin da ya faru.

Wani da ke amfani da shafin Sina Weibo ya ce, ''To ya za yi wanda ba shi da kudi, ya iya biyan mutum 200 kudi domin su halarci bikinsa?''

Yayin da wasu ke ganin cewa ko dai akwai wani dalilin da ya sa shi yake kunyar gayyatar'yan uwansa da abokansa.

Labarai masu alaka