Cristiano Ronaldo ya sake kafa tarihi

Cristiano Ronaldo
Image caption Sau 13 Ronaldo na zuwa wasan kusa da karshe na Champions League

Dan wasan kulob din Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya sake ci wa kulob dinsa kwallaye uku shi kadai a wasan kusa da karshe na gasar Champions League da suka buga da Atletico Madrid.

An dai tashi wasan 3-0 da kungiyoyin suka buga da yammacin Talata a Bernabeu.

Atletico Madrid ta kai hari guda daya tilo wanda tsautsayi ya hana kwallon shiga raga.

Cristiano Ronaldo dai ya kasance dan wasan da ya fi kowanne yawan zura kwallaye a gasar Champions League, a inda ya jefa kwallaye 103 kawo yanzu.

Kuma wannan ne karo na 13 da dan wasan yake zuwa wasan kusa da na karshe na gasar ta Champions League.