'Yadda 'yan jarida ke karbar na goro a Nigeria'

A wasu lokutan akan kashe 'yan jarida a yayin daukar rahoto Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wasu lokutan akan kashe 'yan jarida a yayin daukar rahoto

Ranar uku ga watan Mayu ce ranar da Majalisar dinkin duniya ta kebe a matsayin ranar bikin 'yancin 'yan jarida ta duniya.

A ko ina a fadin duniya,'yan jarida na fuskantar kalubale, musamman a kasashen da ake fama da rikicin siyasa ko na ta'addanci.

Kazalika 'yan jarida musamman mata a wasu lokutan na fuskantar cin zarafi a lokacin da suke gudanar da aikinsu, wani lokaci ma daga wurin abokan aikinsu.

Najeriya, na daga cikin kasashen da 'yan jarida ke da 'yanci, amma a baya-bayan nan, 'yancin ya ragu.

Wani rahoto da kungiyar kare hakin 'yan jarida ta duniya wato Reporters without Borders ta fitar, ya nuna cewa daga cikin kasashen da 'yan jaridu suka fi samun walwala a duniya, Najeriya na mataki na 122 cikin kasashe 180.

Dangane da bikin na wannan rana, wakilin BBC, Yusuf Tijjani ya tattauna da wasu 'yan jarida a Najeriya, kuma ga yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wasu 'yan jarida sun tattauna

Labarai masu alaka