'Yan sanda su yi mana bayani kan kisan Sheikh Jaafar'

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria police
Image caption Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya

A Nigeria, wasu Malaman addinin Musulunci sun kalubalanci rundunar 'yan sandan kasar da ta fito ta yi wa al'umma cikakken bayani game da binciken da suke yi na wadanda suka hallaka fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ja'afar Adam.

Daya daga cikin malaman musulunci a Abujar Najeriya, Sheikh Aliyu Muhammad ya ce hakan ya zama wajibi sakamakon rudanin da ya biyo bayan sanarwar da rundunar ta yi bayan samame da jami'anta suka kai gidan Sanata Danjuma Goje a makon da ya gabata.

'Yan sandan dai sun ce daga cikin abubuwan da suka samu a gidan Gojen har da wani fayil da ke nuna yadda tsohon Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya kitsa kisan da aka yi wa Sheikh Ja'afar.

Tuni dai Sanata Danjuma Goje da Malam Ibrahim Shekarau suka nisanta kansu game da kisan Malamin.

Malam Ibrahim Shekarau ya ma yi barzanar zuwa kotu kan maganar.

Sai dai kuma har yanzu rundunar 'yan sandan ba su uffan ba dangane da kiraye-kirayen malaman na Musulunci.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka harbe Sheikh Jaafar yana sallar Asuba a masallacinsa da ke unguwar Dorayin birnin Kano, shekaru goma da suka shude.