Ana zuzuta rashin lafiyar mijina — Aisha Buhari

AIsha Buhari
Image caption A cikin shekarar 2016 ne Aisha ta fito kafar yada labarai ta soki yadda mijinta ke tafiyar da al'amuran gwamnati

Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta ce ana zuzuta rashin lafiyar mijinta fiye da kima.

A sakonnin da ta wallafa a shafinta na Twitter uwargidan shugaban kasar ta ce Shugaba Muhammadu Buhari mai shekara 74 yana ci gaba da aikinsa da kuma ganawa da manyan jami'an gwamnati.

"Gaskiya ciwon bai yi tsananin da mutane ke zuzuta shi haka ba, don kuwa yana tafiyar da duk al'amuransa da ya saba," in ji Aisha Buhari.

Ta kuma yi godiya ga 'yan Najeriya kan yadda suka nuna damuwarsu da soyayyar da addu'o'i kan rashin lafiyar mijin nata.

Wasu masu fafutuka a Najeriya sun bukaci shugaban kasar ya dauki hutun jinya yayin da ake kara nuna damuwa kan lafiyarsa.

Hakkin mallakar hoto Twitter

A watan Maris, ya dawo daga hutun jinya na mako bakwai a Birtaniya inda aka yi masa magani kan rashin lafiyar da ba a ambata ba.

Lokacin da ya dawo daga gida, ya ce shi bai taba yin irin wannan rashin lafiyar ba a rayuwarsa.

Bai halarci zaman majalisar ministocin kasar ba har sau biyu na baya-bayan nan, bai kuma bai halarci sallar Juma'ar da ta gabata ba a masallacin da ke fadar shugaban kasa.

Aisha Buhari ta janyo ce-ce-ku-ce bara a lokacin da ta zanta da BBC inda ta ce ba za ta goyi bayan mijinta ba a zabe mai zuwa muddin bai yi wa gwamnatinsa garambawul ba.

Da ya ke mayar da martani ga kalaman matarsa, Shugaba Buhari ya ce matarsa ba ta da wani hurumin da ya wuce na 'mai kula da al'amuransa na cikin gida.'

'Ka huta'

Image caption Rashin Lafiyar Shugaba Buhari yana ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Masu fafatuka goma sha uku ciki har da fitaccen lauyan nan, Femi Falana, da mai sharhi kan lamuran siyasa, Jibrin Ibrahim da kuma shugaban kungiyar Transparency International Nigeria, Auwal Musa Rafsanjani, sun fitar da wata sanarwar da ke cewa rashin bayyanar shugaban a zaman majalisar ministoci da kuma na sallar Juma'a sun ruruta jita-jita kan halin lafiyar shugaban kasar.

Sun ce dole su kira shugaban ya bi shawarar likitocinsa ta hanyar daukar hutun jinya ba tare da bata lokaci ba.

Labarai masu alaka