An kai mummunan hari kan tawagar Nato a Afghanistan

Tawagar nato Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai harin ne a tsakiyar birnin Kabul

Jami'ai sun ce harin kunar bakin wake da aka kai kan tawagar Nato a Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas a birnin Kabul.

Mai magana da yawun gwamnati ya ce wadanda lamarin ya ritsa da su fararen hula ne. Kuma mutum 25 sun samu raunuka, ciki har da sojojin Amurka uku.

An kai harin ne kan tawagar motocin soji, kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke kasar da safiyar ranar Laraba.

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar dai na kasar tun shekarar 2015 kuma a baya-bayan nan ta dauki alhakin hare-hare da dama a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa motocin soji biyu ne, tare da wasu masu yawa dake wucewa suka lalace yayin harin. Kuma kofofin motoci sun yi ta ballewa zuwa wuri mai nisa daga inda lamarin ya faru.

Hakkin mallakar hoto Ronald Grant
Image caption Jami'ai sun ce mafiya yawan wadanda lamarin ya rutsa da su fararen hula ne

Harin dai na zuwa ne mako uku bayan Amurka ta girke wani babban garkuwar makami mai linzami, wanda aka fi sani da "uwar boma-bomai", a wani wuri da 'yan IS ke amfani da shi a kasar, wanda ya hallaka 'yan tawaye masu yawa.

A halin yanzu dai, Amurka na tattauna yiyuwar tura karin sojoji zuwa Afghanistan, inda yanzu ayyukan 'yan ta'adda ke kara ta'azzara.

Labarai masu alaka