Cinikin wayar iPhone ya ja baya sosai a kasuwanni

Pedestrians walks past Apple logo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin iPhones ya fitar da wani sakamakon cinikinsa wanda a ciki yake cewa kamfanin bai yi sayar da wayoyin da yawa ba a watanni ukun farko na shekarar 2017, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kamfanin da ke jihar California a Amurka wanda yake dab da fitar da sabuwar wayar iphone ta yayi a cikin wannan shekarar, ya ce ya sayar da wayar iphone miliyan 50.8 ne kawai a wannan tsakani, inda hakan ya ragu da kashi daya cikin 100 idan aka kwatanta da bara a daidai wannan lokaci.

Shugaban kamfanin Tim Cook, ya zargi jan bayan cinikin da cewa masu sayen wayar suna jiran a sake fito da wata sabuwar iPhone din ne.

Hannun jari a kamfanin ya fadi da kusan kaso biyu cikin 100 a bayan sa'o'i kadan da bude kasuwar hannayen jari, bayan da aka sa ran za a samu kasuwa mai kyau.

Kamfanin ya ba da rahoton cewa, an samu karin kudin shiga a kamfanin da kashi 4.6 cikin dari zuwa billiyan 41, inda hakan ya gaza da hasashen da masu sharhi suka yi.

Ja bayan da aka samu a kasuwannin wayar ya fusata masu cinikin, wadanda suka hada da manhajar Apple Pay, da iCloud, da App store, wanda aka ba da rahoton ya karu da kashi 18 cikin dari zuwa dala biliyan bakwai.

Har ila yau Mr Cook ya gano cewa za a kara samun cinikin Agogon kamfanin , "Apple Watch," da AirPods, da kuma Beats earphones.

Duk da cewa an samu ja baya a kasuwanni, har yanzu ana samun kudin-shiga daga wayoyin iPhones na kaso daya cikin dari zuwa billiyan 33.3, saboda sayan manyan wayoyin, musamman mai tsadar ciki kirar iPhone 7 Plus.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sharhi daga wakilin BBC kan al'amuran fasaha a arewacin Amurka Dave Lee

A kalla wannan ne al'amari mara armashi na abun da kamfanin ya samu a shekara, tun bayan da aka gama bikin sallar kirsimetin bara.

Sai dai koma-bayan da aka samu fiye da yadda aka sa rai a cinikin iPhone ya sa masu zuba jari ba su ji dadi ba, bayan sa rai da karuwar cinikin sosai ya sa farashin hannayen jarin kamfanin sun yi tashin da ba su taba yi ba ranar Talata.

Har ila yau, Tim Cook ya shaidawa masu zuba hannun jari cewa, yana jin dadin ci gaba da bunkasar kayayyakinsu, kamar su manhajar Apple Music, da Apple TV, da iTunes da sauransu.

Yanzu haka za a sa ido don ganin me zai faru nan gaba cikin shekarar nan.

A bikin cika shekaru goma da kamfanin zai yi, ana sa ran za a samu karin jama'a masu sayar da wata sabuwar wayar da za mu fito da ita.

Labarai masu alaka

Karin bayani