An ceto zabiyar gwaggon biri a Indonesia

This handout picture taken on April 30, 2017 and released on May 2, 2017 by the Borneo Orangutan Survival Foundation shows a rare albino orangutan that was saved from villagers in Kapuas Hulu, on the Indonesian side of Borneo islan Hakkin mallakar hoto AFP/BOSF
Image caption Gwaggon birin yankin Bornea na fuskantar mummunan hadari

Kungiyar kare hakkin dabbobi ta kasar Indonosiya tana kula da wani zabiyar gwaggon biranya wanda ba a faye samun irin su ba da aka ceto daga hannun wasu mutane.

Gwaggon biranyar, mai farin gashi da kuma kwayar ido shudi, an kama ta ne a wani kungurmin kauye na kasar Indonisiya, a yankin tsibirin Borneo.

Gidauniyar masu ceto gwaggon biri ta Borneo ta ce, an saka gwaggon biranyar a cikin keji na tsawon kwana biyu "amma har yanzu tana nuna halayyar hauka."

Gidauniyar ta ce, nan ba da dadewa ba za a saki dabbar ta koma daji.

'Rashin son haske'

Gidauniyar BOS, ta shaidawa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa, ba a faye samun zabiyan gwaggon biri ba, kuma wannan ne karo na farko da kungiyar ta kama irin su a cikin shekara 25 na tarihin kafuwarta.

Kungiyar ta ce, ta tabbatar da cewa gwaggon biranyar zabiya ce, bayan da aka yi mata gwaje-gwaje, aka kuma gano cewa idanuwanta ba sa son haske sosai.

Dabbar, wada aka yi yakinin cewa za ta kai shekara biyar, an ajiyeta a cibiyar kula da dabbobi ta kungiyar, mai dauke da kusan gwaggon biri 500.

Kungiyar kare halittu ta duniya, wato IUCN ta bayyana gwaggon birin da ake samu a yankin Bornean a matsayin, "wadanda suke matukar fuskantar barazana."

IUCN ta ce, an samu raguwar irinsu da sama da kashi 60 cikin 100 a tsakanin shekarar 1950 da shekarar 2010, sakamakon lalacewar mazauninsu da kuma farautarsu da ake yi, ta kuma tabbatar da cewa ana zaton samun kashi 22 cikin 100 a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2025.

Hakkin mallakar hoto AFP/BOSF
Image caption Birin ya ji rauni a hancinsa a kokarin da yake na kwacewa daga wadanda suka kama shi

An kiyasta cewa, a kalla gwaggon biri 100,000 ke zaune a kan tsibirin Borneo, wadanda suke bazuwa tsakanin kasar Malaysia da Brunei, da kuma Indonesia.

Gidauniyar BOS ta ce, wata kila za a iya samun zabiyan gwaggon biri masu yawa a kan tsibirin.

Jaridar Jakarta Post ta rawaito shugaban Jamartin Sihite yana cewa," Akwai gwaggo birin da suke zaune a dajin, kuma daga wurinsu ne gwaggon biri zabiya suka gaji wannan halittar."

Labarai masu alaka

Karin bayani