An ba da belin tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu

Mu'azu Babangida Aliyu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mu'azu na cikin gwamnonin masu fada-aji a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan

Rahotanni daga jihar Neja a arewacin Najeriya na cewa kotu ta bayar da belin tsojon gwamnan jihar, Mu'azu Babangida Aliyu, da tsohon dan takaran gwamnan jihar karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Umar Gado Nasko.

Mai Shari'a Aliyu Maiyaki na babban kotun jihar ne ya bayar da belin Babangida Aliyu da sharadin cewa zai bayar da kudi naira miliyan 150, zai kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa wadanda suka mallaki kadarar da ta kai kudi naira miliyan 200 a wurin da ke karkashin ikon kotun.

Ya kuma bayar da belin Umar Gado Nasko da sharadin cewa zai ba da kudi naira miliyan 100 da mutum biyu da za su tsaya masa da suka mallaki naira kadarar da ta kai kudi naira miliyan 150 a wurin da ke karkashin ikon kotun.

Hakan na nufin za a ci gaba da shari'ar a kotun tsakanin hukumar EFCC da wadanda ake kara.

A watan da ya gabata ne hukumar da ke yaki masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) ta gurfanar da Mu'azu Babangida Aliyu da Umar Gado Nasko a gaban kotun kan zargin yin sama da fadi da naira biliyan 4.568.

Lauyan wadanda ake zargin ya nemi kotun ta bayar da belinsu a ranar 25 ga watan Afrilu, amman lauyan hukumar EFCC ya ce ana ajiye wadanda ake zargi a gidan wakafi ne da zarar kotu ta karbi kara.

Saboda haka, sai alkalin ya ba da umarnin a tsare Babangida Aliyu da Umar Gado Nasko a kurkuku zuwa ranar Laraba 3 ga watan Mayu, domin ya yanke hukunci kan belin da lauyan wadanda ake zargin ya nema.

Mu'azu Babangida Aliyu ya mulki jihar Neja tsawon shekara takwas, kuma ya yi shekara hudu yana shugabancin kungiyar gwamnonin arewacin tarayyar Najeriya.