'Da haƙar daiman na biya kuɗin makarantata'

diamond Hakkin mallakar hoto Image copyrightGETTY IMAGES
Image caption Hakar diaman ba abu ne mai sauki ba

Na taso a kudancin kasar Saliyo mai arzikin daiman don haka abu ne da matasa suka saba yi.

A da can ma da yanzu ma babu isasun aikin yi don haka da aikin hakar ma'adinai matasa ke dogaro.

Sun shawo kan matasa da dama sun bar makaranta amma ni na kan yi aikin hakar ma'adinai a lokacin da muke hutun makaranta sai kuma a kwanakin karshen mako.

Mazauna yankin Kono na da yawa saboda yawan diaman da ake samu kusan ko ina idan ma mutum ya yi sa'a a haka kawai sai ya tsinta.

Iyayena tare da dubban mutane daga sassan kasar, har da 'yan Gambia da Mali da Senegal da ma 'yan Lebanon na zuwa Kono da fatan samun sa'a.

Kanta a hannu

A nan na girma kuma aikin da na yi mai wahala ne sosai a lokacin.

Ina hako rami a kogi don na samo tsakuwa sai na fitar da tabo na nemo diaman.

Gatari da shebir da nake amfani da su kan sa tafin hannayena su yi kanta, sannan yawan tatar da nake yi kan sa faratana su yi karfi inda suke yawan karyewa ko ma su mutu.

Kuma saboda ina yawan daukar buhunhuna cike da duwatsu, kusan ko da yaushe kaina da wuyana su na min ciwo.

A wasu lokutan ana ganin burbushin diaman a kasa a wasu bangarorin Kono har ma mutane su rika tsinta wasu idan aka yi ruwan sama.

Na taba tsintar wasu duwatsu sau daya ko biyu haka a Bumpeh, garin da aka haife ni. A lokacin ban san darajarsu ba, amma dai na samu kudin da zan batar na tsawon mako guda.

Bayan na yi jarrabawar karshe ta barin makaranta, sai na koma ina aikin hakar ma'adinai domin na biya kudin karatun jami'a.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tauraron Sierra Leone, an gano diaman mafi girma a shekaarar 1972

Baya ga hakar ma'adinai da nake yi a Kono, na kuma tafi Tongo a makwabciyar yankin Kenema. A can, na gano cewar masu aikin hakar ma'adinai na aiki ne kamar leburori.

A yanayin aikin da aka saba yi shekara da shekaru, ko wacce kungiya na da uban gidanta da ke kula da su. Shi ke da alhakin ba su abinci da muhalli da magani.

Amma a lokacin da nake can, an tsara ka'idojin ne ta yadda mutum na da tabbas din abinci sau daya kawai amma fa kar ka tambayi ko ya ya dandanon abincin yake.

Mu kan kwanta ne a kan dandabaryar kasan wani daki ko a soro inda sauro da kudin cizo ke cizonmu. A bangaren lafiya kuwa, Panadol ne kawai maganin da ake ba mu idan har muka yi rashin lafiya.

Akwai kuma mai bayar da tallafi - shi ne mutumin da yake bai wa shugabanmu kudi.

Ba safai muke ganinsa ba. Dan kasuwa ne kuma yana harkar diaman kuma shi ke ba mu kayan aikin hakar da kuma alawus-alwus a ko wannne wata.

Kamar dai ni, akasarin masu hakar ba su sani ba kuma har yanzu ma basu san darajar diamand din ba. Saboda haka sai su hade kai su rika cutarmu a kan farashin.

Abubuwa masu kyalli

Hakkin mallakar hoto OLIVIA ACLAND
Image caption Sai kana gani sosai zaka iya gano diamond

Mu biyu ne a zaune muke tata, sai mutum na uku na kwasar duwatsu. Ina ta tata a kasan ruwan domin na wanke tabon da ke jikin duwatsun.

Sai kawai na hango wani abu mai kyalli a tsakiyar duwatsun da nake tacewa.

A lokacin ban tabbatar ba ko diaman ne ko kuma corundum ne ba, wani dutse mai kyalli da bashi da daraja sosai. Sai na dago matatar domin na tabbatar.

Sai na saka hannu na dai-dai inda dutsen yake domin na ware shi daga cikin sauran duwatsun da kasar.

Sai kawai na ji gabana ya fadi. A hankali na radawa abokan aikina: "na diaman" wanda hakan ke nufin " diaman ne".

A hankali na fada saboda tsoron kar wani na nesa ya jiyo ni.

Yarpo, abokin aikina, ya saki bokitin da ke hannunsa domin ya tabbatar da abin da na tsinta. Ya amince cewa diaman ne.

Duk sai muka zubar da kayan aikinmu muka shige can cikin ciyayi. Sai muka gudu kafin ma wani ya kama mu.

Image caption Akasarin masu hakan ba su sani ba kuma har yanzu ma basu san darajar diamonds ba

Sai kawai muka boyewa shugabanmu mu ka sayarwa wani dilan daiman a kan kudin kasar leon 100,000. Ban tabbatar da darajar kudin ba a dallar Amurka a shekarar 1991, amma dai ba wai wasu kudi ne masu yawa ba.

Ni ne mafi karancin shekaru, amma ragowar masu hakar guda biyu sun kyautata min. Mun raba kudin sai suka bani 34,000 leone wanda ya dan fi yawan nasu.

Ba kamar yadda ragowar mahaka suke yi ba, ni ban bata kudin da na samu kan sayan sabbin kayan sakawa ba.

Da ma can nasan me nake so na yi da kudin nawa - na biya kudin shekarar farko na jami'a wanda kusan 24,000 leone ne.

Burina ya cika

A lokacin ina jiran sakamakon jarrabawata ta fito, don haka sai na bai wa 'yar uwar mahaifiyata kudina ta kara ta ja jari ta yi kasuwanci.

Hakkin mallakar hoto UMARU FOFANA
Image caption Wannan ne daya daga cikin hotunan da Umaru yake da shi kawai na lokacin da yake jami'a

Sai na koma na mayar da hankali kan hakar ma'adinan, amma sai ya kasance wannan ne karo na karshe da zan samu wannan sa'ar a matsayina na mai haka.

Na dade ina so na zama dan jarida saboda an haife ni a cikin masu yawan sauraron shirye-shiryen BBC.

Mahaifina bai taba zuwa makaranta ba amma kuma ya matukar sabawa da sauraron BBC.

Sai dai kwalejin Fourah da ke Saliyo ba ta koyar da aikin jarida a lokacin. Don haka sai na yanke shawarar na karanta Turanci da Faransanci.

Na kammala karatun digiri na fara aiki a matsayin dan jarida.

Kamar dai ni, yarana sun taso da BBC, sai dai muryata na cikin muryoyin da suke saurare.

Labarai masu alaka