Likimo ya banbanta da barci — Ganduje

Kwankwaso da Ganduje Hakkin mallakar hoto Kano State Government
Image caption Kwankwaso da Ganduje sun shafe shekaru suna tafiya tare a siyasance

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai banbanci tsakanin likimo da barci.

Masu hammayya dai na yawan sukar gwamnan da yin barci a lokacin aiki.

A baya-bayan nan hotunan gwamnan suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda Ganduje yake 'barci' a wuraren taruka.

Hakan ne yasa gwamnan kasa yin shiru har ya mayar da martani, a inda ya nemi rarrabe tsakanin tsaki da tsakuwa.

To amma hakan ya kara zafafa muhawara tsakanin bangaren gwamnan da ake kira Gandujiyya da kuma tsagin tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya.

Mabiya Kwankwasiyya sun ce likimo bacci ne, a inda magoya bayan Gandujiyya ke cewa mai basira ne kawai yake yin likimo.

Wannan dai na nuna irin yadda rabuwar kai tsakanin 'yan jam'iyyar APC a jihar Kano ke kara tsananta.

Jim kadan dai bayan da gwamna Rabi'u Kwankwaso ya mika wa Abdullahi Ganduje mulke wanda tsohon mataimakinsa ne ake ta samun rarrabuwar kai.