US: Malaman addini za su fara shiga harkokin siyasa

Donald Trump ya ce ya sha yin korafi kan dokar hana malaman addini da na coci shiga harkokin siyasar kasar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Donald Trump ya ce ya sha yin korafi kan dokar hana malaman addini da na coci shiga harkokin siyasar kasar

Fadar White House ta Amurka, ta ce Shugaba Donald Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta kwaye wa malaman addini da na coci-coci takunkumi shiga a dama da su a harkokin siyasa.

Dokar dai za ta zamo gyaran fuska ga dokar da ta hana malaman addini nuna goyon bayansu kai tsaye ko kuma hamayya ga wani dan takara.

Shugaban na Amurka, Donald Trump dai ya sha yin korafi kan wannan dokar, sai dai kuma sake dokar kacokan na bukatar hannun majalisar dokoki.

Ana dai ganin sanya hannu a dokar na daya daga cikin sauye-sauyen da Mista Trump ke son yi ga tsare-tsaren mutumin da ya gada wato, Barrack Obama.

Mista Obama dai ya takaita wa malaman addini shiga a dama da su kai tsaye a siyasa.

Dokar wadda za a sanya mata hannu ranar Alhamis, za ta bai wa malaman na addini 'yanci kamar kowa, sannan kuma su samu damar sukar batutuwa kamar luwadi da madigo da kuma hana daukar ciki.

Labarai masu alaka