Macron zai iya kayar da Le Pen a zaben France

Le Pen a hagu da Macron a dama
Image caption Marine Le Pen da Emmanuel Macron sun fafata a mahawara

Dan takarar neman shugabancin Faransa na jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi, Emmanuel Macron, ya kara samun tagomashi a tsakanin masu zabe, bayan wata zazzafar mahawara da suka kafsa da 'yar takara mai tsattsauran ra'ayi, Marine Le Pen, a gidan talbijin.

'yan takarar dai sun kwashe fiye da sa'a biyu suna mahawara a inda suka yi ja cin mutuncin juna.

Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun kwashe awa biyu da rabi suna jifan juna da zarge-zarge iri-iri da kuma cin mutuncin juna.

Marine Le Pen ta so ta kwance wa abokin karawartata zane a kasuwa ta hanyar jifan sa da abun da talakawa za su kyamace shi wato shi dan takarar masu fada-aji ne.

Le Pen ta ce "Zabin da Faransa ta yi a siyasance zai bayyana mista Macron dan takarar kasashen duniya ne masu san sarayar da 'yancin tattalin arzikinmu kuma maketata ga talakawa da mista Hollande ke kitsawa."

To amma hakan bai yi nasara ba domin kaso biyu bisa uku na 'yan kwallo sun riga sun yanke cewa Emmanuel Macron ya fi gamsar da su a mahawarar, bayan da ya fito da kwan-gaba-kwan-baya kan manufofin 'yar takarar na tattalin arziki.

Macron ya tambayi Le Pen "Wace ce ke yada fargaba a zukatan 'yan faransa? Ke ce. Wace ce take yin yawo da hankalin al'ummar faransa kan ta'addanci? Idan ban da Ke. Jama'a ku kalli fargaba da kanta wadda kuma take ci da ceto da ita, ga ta nan a zaune a gabana."

Ya kuma kara da cewa misis Le Pen cakwaikwaiwa ce mai yawan zance amma babu komai a zantuttukan nata illa hauma-hauma.

Masu lura da al'amura dai na yi wa wannan mahawara kallon wani danba da aka dasa wanda ba zai haifar wa kasar Faransa alheri ba a siyasance, bilhasali ba suna ganin mahawarar ta zubar da kimar siyasar kasar.

Mahawarar dai ta fito da irin zafin hamayyar da ke tsakanin 'yan takarar biyu, fili.

Za dai a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugabancin Faransa a ranar bakwai ga watan Mayu.