Nigeria: Kotu ta ba da belin Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido
Image caption Jami'iyyar PDP ta Sule Lamido ta ce kamen nasa siyasa ce kawai, abin da APC ta musanta

Wata kotun majistare a Najeriya ta ba da belin tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda ake zargi da laifin tunzura jama'a, zargin da ya musanta.

Kotun, da ke Dutse babban birnin jihar, ta bayar da belinsa ne bisa la'akari da kimarsa a cikin al'umma.

A ranar Talata ne aka gurfanar da Sule Lamido a gaban kotun bayan da gwamnatin jihar ta kai kararsa bisa zargin yin kalaman tunzura jama'a.

An tuhume shi da aikata laifuka hudu da suka danganci neman tayar da zaune tsaye, amma tsohon gwamnan ya yi watsi da zargin.

Lauyoyinsa sun bukaci a bayar da belinsa, sai dai lauyoyin gwamnati sun ki yarda da hakan, inda suka nuna wa alkalin cewa laifukan da ake tuhumarsa a kansu sun yi girman da bai kamata a bayar da belinsa ba.

Kotun ta sanya ranar 5 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraron shari'ar.

A ranar Lahadi ne 'yan sanda suka kama tsohon gwamnan a birnin Kano bayan gwamnatin jihar ta zarge shi da yin kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina.

Sai dai magoya bayansa sun ce jagaoran nasu kawai ya cewa jama'a ne, "su kasa, su tsare sannan su kuma raka akwatinan zabensu" a zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihar.

Shi dai Sule Lamido, wanda ya mulki jihar daga shekarar 2007 zuwa 2015, ya yi fice wurin sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

Jam'iyyar PDP ta ce kamen nasa wani yunkuri ne na dakile kaifin 'yan adawa a kasar, sai dai gwamnatin APC ta musanta hakan.

Labarai masu alaka