An harbe matashin ministan gwamnatin Somalia

Abdullahi Sheikh Abas beat a state minister to become an MP
Image caption Abdullahi Sheikh Abas ya girma a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Jami'ai a Somaliya sun bayyana cewa wasu dakarun rundunar tsaron kasar sun harbe wani ministan gwamnati mai shekara 31 a bisa kuskure, inda suka yi zaton cewa ko dan kungiyar Al-Shabab ne.

Jami'an sun kara da cewa, an harbe shi ne a cikin motarsa a kusa da fadar shugaban kasar, a birnin Mogadishu.

Gidan rediyon gwamnatin kasar ya bayar da rahoton cewa, Shugaban kasar ya katse ziyarar da yake yi a kasar Ethiopia a yayin da ya samu labarin kisan Abdullahi Sheikh Abas.

Mista Abas ya girma ne a wani sansanin 'yan gudun hijira ya kuma zama matashin dan majalisar kasar a watan Nuwamba, sannan kuma ya zama Minista a watan Fabrairu.

Tun lokacin da aka tumbuke shugaban da ya dade yana mulkin kasar Siad Barre a shekarar 1991, kasar ke fama da rikici.

Yanzu haka kasar na yaki da masu kaifin kishin Islama na kungiyar al-Shabab, wadanda suke da alaka da kungiyar al-Qaeda.

Jami'an tsaro na ci-da-zuci

Wani babban jami'in dan sanda, Major Nur Hussein, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa, dakarun tsaron da ke sintiri ne suka ga motar ta tare hanya, sai suka yi tunanin cewa ko dan tawaye ne a ciki, inda hakan yasa suka budewa motar wuta.

An rawaito inda mai magana da yawun magajin garin birnin Mogadishu Abdifatah Omar Halane, yana cewa, "An kashe Mista Abas ne a kan rashin-sani, inda suka budewa motarsa wuta. Muna addu'ar Allah ya jikansa."

Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo ya ce, ya umarci shugabannin jami'an tsaro,"da su gaggauta kawo karshen wannan bala'i", kuma su tabbatar da cewa sun gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan abu.

Gidan rediyon gwamnatin kasar ya bayar da rahoton cewa, Ministan yada labarai Abdirahman Osman ya ce, an kama mutane da dama, sai dai ba su bayar da wani bayani ba.

Sharhi

Wakili BBC da ke Somaliya Abdullahi Abdi, ya ce, wasu lokutan jami'an tsaro suna ci-da-zuci, a baya sun sha harbe jami'an gwamnati ko kuma su kashe junansu a bisa kuskure.

Ya kara da cewa, "Amma za ta iya yiwuwa Mista Abas, ministan ayyuka na kasar, shi ne jami'i mafi girma da aka taba kashewa.

Bayan da shugaban kasar ya samu nasara a zabe ne, ya nada shi minista a watan Fabrairu.

Shugaba Farmajo ya yi alkawarin inganta tsaro da kuma kafa gwamnati mai tasiri a kasar.

Yanzu haka yawancin sassan kasar na karkashin ikon al-Shabab.

Mista Abas ya girma a sansanin 'yan gudun hijra na Dadaab da ke kasar Kenya, wanda yake dauke da dubban daruruwan 'yan kasar Somaliya da suka gujewa yunwa da rikici.

Labarai masu alaka