An dauke wuta gaba daya a Ghana

Ghana
Image caption An dauke wata gaba daya a kasar Ghana

Shugaban kamfanin wutar lantarki na Ghana ya ce an samu matsala da na'urorin da ke samar da wutar lantarki na kasa, al'amarin da ya jawo aka dauke wuta a duk fadin kasar a ranar Laraba da daddare.

A lokacin da shugaban zartarwa na kamfanin lantarki na GRIDCo William Amuna, ke hira da gidan rediyo na Citi FM, ya ce, ''An dauke wutar da misalin karfe 9:40 na dare kuma dukkan na'urorinmu sun lalace'' .

Ya kara da cewa yana sa ran za a dawo da wutar da karfe 10 na safiyar ranar Alhamis, sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari ba a kawo wutar ba.

Al'ummar kasar dai suna ta korafi kan al'amarin, inda suka ce hakan ya jawo musu matsala ta bangaren sadarwa da sauran al'amura.

Wasu sun shaidawa BBC ta wayar tarho cewa, yanzu haka akwai cunkoson motoci a tituna saboda rashin wutar ya sa danjojin da ke bayar da hannu ba sa aiki.

Kazalika sun koka kan yadda kayan abinci da suka adana a firji suka fara lalacewa, saboda mafi yawan masu karamin karfi a kasar ba su da halin ajiye janareto.

Da yawan masu kananan sana'o'i da suke amfani da wutar lantarki kamar masu aski da gyaran gashi da sauran su sun ce ba sa samun cinikia ranar Alhamis don ba wutar da za su yi aikin da ita.

Mista Amuna dai ya ce, "Wannan ba tsarin dauke wuta da muka saba da shi ba ne.

An taba dauke wuta gaba daya a kasar a watan Janairun 2016 saboda matsalar naurori.

Hukumoni na gudanar da bincike a kan dalilin da ya janyo wannan matsala, amma yana ganin cewa walkiya da tsawa ne ya haddasa hakan.

A ranar Laraba ne ake yi ruwa da walkiya mai tsanani a jihar Volta, inda babbar Hukumar da ke samarwa kasar wutar lantarki na VRA yake.

Labarai masu alaka