Ka san rigar mama da ke gano cutar kansa?

Mexico Hakkin mallakar hoto Higia Technologies
Image caption Rigar mama dake gano cutar kansa.

Wani matashi a Mexico ya kirkiro wata rigar mama da ke iya gano cutar daji. Abar tambaya a nan ita ce tana aiki? In kuwa tana yi , ta yaya?

Julian Rios Cantu mai shekara 18 ya kirkiro wata rigar mama da ya ce zata iya gano cututtukan mama.

Mista Cantu da abokannansa uku da suka kafa kamfani tare, suka kirkiro wannan rigar mama da ake kira Eva.

Sun samu kudi masu yawa don fara gwaje-gwaje kuma a wannan mako suka lashe kyautar dalibai 'yan kasuwa na duniya na Global Student Entrepreneur Awards.

Kamfaninsu mai suna Higia Technologies, ya samu nasara kan wasu matasa yan kasuwa na sassan duniya inda suka samu kyautar dala 20,000 da suka yi amfani da shi wajen kirkirar rigar maman.

Ta yaya wannan rigar mama zata gano ciwon daji ?

Ciwon daji na canza yanayin jikin mutum saboda yawan jinin dake gudana a jikin dan adam. Manufar rigar mama ta Eva, ita ce zata lura da yanayin jini mutum, sai ya nadi sakamakon yanayin a wata manhaja wanda zai ankarar da bai sanye da ita idan har akwai alamun damuwa.

An bukacin matan da za su yi amfani da wanna nrigar maman su saka ta na tsawon sa'a guda zuwa guda da rabi a kowanne mako domin samun hakikanin awon da manhajar ta yi..

Ba a gwada wannan rigar maman ba tukuna kuma za a bukaci a yi gwaji a asibitoci kafin masana kan ciwon daji su fara amfani da ita ta hanyar gano cutar.

Jami'a a cibiyar bincike kan ciwon daji, Anna Perman, da ke Britaniya ta shaidawa BBC cewa '' Mun san cewa kwayoyin cutar kansa na da wani irin tsari na yadda yake gudanar da jini na daban, amma kuma mun san cewa ba lallai bane ya zamana yawan gudanar jini cikin jikin dan adam ya zama wani abu da za a dogara kan cewa akwai alamar mutum na dauke da cutar kansa.

'' A halin yanzu babu wata shaida dake nuna cewa wannan rigar mama zata iya gano cutar kansa don haka ba za a bai wa mata shawarar su yi amfani da fasahar da ba a yi gwaje-gwaje mai inganci a kai ba.

Misis Perman ta kara da cewa '' Yana da kyau yara matasa su rika kirkiro hanyar gano cutar kansa. Haka kuma yana da muhimmanci a samu masu ilimin kimiya su rika yin gwaji ta yadda za a iya amfani da shi wajen gano masu dauke da cutar kansa.

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba