Wani ya rubuce Kur'ani a shafi daya a Masar

Saad Mohammed Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saad Mohammed ya shafe shekara uku yana kofar qur'ani ka wannan doguwar takardar

Rubutun Kur'anin, wanda Saad Mohammed ya yi a kayace da hannusa na da tsayin ma'aunin mita 700, wanda hakan ke nufin idan aka warware takardar da ya yi rubutun a kai, tsayinta zai kai tsayin ginin Empire State Building da ke birnin New York.

Ya zuwa yanzu, Mohammed , wanda ke zaune a garin Belqina da ke arewacin birnin Alkahira, da kudinsa ya yi amfani wajen yin wannan aiki. Amma yana da ka kyakkyawan fata kan rubutun kur'anin da ya yi.

Ya yi amanna cewar tsayin takardar da ya yi rubutun a kai ta kai tsayin da za a iya kafa tarihinsa a cikin littafin Guinness World Records, da ake adana bayanan abubuwa masu ban al'ajabi.

Ya zuwa yanzu dai, Guinness World Records ba shi da tarihin kur'ani mafi tsayin wanda aka rubuta da hannu.

Amma idan har yana so ya cika burinsa na shiga Guinness World Record, yana bukatar taimakon kudi kafin ya shiga.

Mohammed ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Wannan Kura'anin na da tsayin ma'aunin mita 700 kuma shakka babu takarda ce mai tsayi sosai.

Ya kara da cewa, "Da kaina na biya kudin wannan aikin a cikin shekara uku kuma ni ba mai kudi ba ne. Ba ni da wata kadara ko wani abu."

Kur'anin da yafi dadewa a duniya a hukumance a cewar Guinness World Record, shi ne Kur'anin Mushaf na Othman, wanda aka rubuta a shekarar 655 kuma mallakin Khalifa Othman ne.

A yanzu an adana fallaye 705 na Kur'anin a kasar Uzbekistan.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsayin Kur'anin ya kai tafiyar minti biyar
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sa'ad Mohammed ya kuma rubuta wasu littittafan daban

An gano wani wanda yake gasar rubutun kur'anin da hannu a Afghanistan a shekarar 2012. Ya fi tsayin mita 2.2 da fadin mita 1.55, yana dauke da shafuka 218 na kayataccen rubutun kur'ani kuma an nade shi a cikin fatar akuya 21.

An dauki tsawon shekara biyar kafin a kammala rubutun kur'anin mai nauyin kilogiram 500, amma da alamun har yanzu ba a kaddamar da shi a littafin Guinness Book of Records ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsadar takardar da ya rubuce qur'anin a kai ma kawai abin dubawa ne

Babu wanda ya taba ikirarin hada kur'ani mafi kankanta.

Duk da haka, a shekarar 2012 wani mazaunin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya yi ikirarin hada kur'ani mai tsayin sentimita 5.1 da fadin sentimita 8 da shafuka 550.

Labarai masu alaka