Kuna ganin ya kamata malaman addini su shiga harkokin siyasa?

Wasu na ganin ya kamata malamai su shiga a dama da su a harkokin siyasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu na ganin ya kamata malamai su shiga a dama da su a harkokin siyasa

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka da za ta bai wa malaman addini damar shiga a dama da su a harkokin siyasa.

A kasashe irin su Najeriya da Nijar ma, wasu na ganin shigar malamai harkokin siyasa zai taimaka wajen inganta rayuwar jama'a.

Sai dai a gefe guda, wasu na ganin hakan zai rage irin martabar da suke da ita a idanun jama'a inda za a rika zaginsu, kamar yadda siyasa ta gada.

Kuna ganin ya kamata malaman addini su shiga harkokin siyasa? Ko dai su tsaya a matsayinsu na masu yi wa al'uma wa'azi?

Mun daina karbar tambayoyi ta wannan shafin. Mun gode.

Labarai masu alaka