Ungozomar da ke ceton jarirai mata-maza daga barazanar kashe su

Kenya Hakkin mallakar hoto Charlotte Edey

Shekara biyar da suka shude, wata unguwar zoma a kasar Kenya ta karbi haihuwar wani jariri mai al'aurar maza da mata. Mahaifin jaririn ya umarce ta da ta kashe wannan jaririn, amma sai kawai ta boye shi kuma ta raine shi a matsayin nata. Bayan shekara biyu, irin wannan lamarin ya sake faruwa - dalilin da ya tilasta mata tserewa domin ta ceci rayuwar yaran.

Ita dai Zainab ta saba karbar haihuwar jarirrai. Ita unguwar zoma ce a karkarar kasar Kenya, kuma ta karbi haihuwar jarirai masu dama. Amma bata taba ganin irin jaririn da ke gabanta ba a halin yanzu.

Tun da farko haihuwar ta zo da gardama, amma ba wani lamari ne da ya gagari Zainab ba. Cibiyar jaririn ce ta nade kansa, sai da ta yi amfani da ludayin ice kafin ta iya cire shi.

Bayan ta bude hanyoyin shan iska, sai ta wanke jaririn kuma ta yanke masa cibi. A lokacin ne ta ga wani abin da bata taba gani ba.

Tace: "Da na duba don in tantance namiji aka samu ko mace ce, sai naga wasu abubuwa guda biyu - wannan jaririn na da al'aurar maza da ta mata."

A maimakon ta bayyana ma iyayen jaririn abin da aka samu, kamar - "Namiji ne" ko "Mace ce" - sai Zainab ta mika jaririn ga uwarsa ta ce mata, "Ga jaririnki."

Da mahaifiyar wannan jariri ta gane irin halin da ake ciki, hankalinta ya tashi. Amma da isowar mijinta, bai yi wata-wata ba game da matakin da ya ke son a dauka.

Ya bukace ni da in mika masa yaran domin ya hallaka shi ta hanyar jefa shi a cikin tafki - ni kuma na fada masa cewa ba zan taba yarda da haka ba.

Zainab Unguwar zoma

"Ya fada min cewa, 'Ba zamu iya komawa da wannan jaririn gidanmu ba. Muna bukatar a kashe wannan jaririn.'

Ni kuma na sanar da shi cewa ai jaririn halittar Allah ne wanda bai kamata a kashe shi ba. Amma sai ya matsa. Daga baya sai na gaya masa 'Ka bar jaririn tare da ni, zan kashe maka shi.' Amma ban kashe jaririn ba. A madadin haka sai na raine shi."

Mahaifin wannan jariri ya koma wajen Zainab don ya tabbatar da ta cika alkawarin da tayi masa. Sai ta boye jaririn kuma ta hakikance da ta kashe shi. Amma ta san wannan ba zai iya dorewa ba har abada.

"Bayan shekara guda, sai kawai iyayen jaririn suka sami labarin cewa yana da nan da rai kuma suka tambaye ni," in ji Zainab. " Sun yi min kashedin kada in taba bayyana cewa jaririn nasu ne. Sai na amince kuma tun wancan lokacin nake rainon yaron a matsayin nawa."

Mataki ne mai wahala - kuma mai hatsari

A yankin da Zainab ta fito, har ma da wasu yankunan masu dama a Kenya, ana ganin irin yara mata-maza a matsayin abin kyama, abin da kan iya jawo tsinuwa ga iyalansu har ma da makwabtansu. Wannan abu da Zainab ta yi ya saba wa al'adun gargajiya na al'umomin wanda zai iya jawo mata zargi a duk lokacin da wani abu maras kyau ya faru.

Wannan lamarin ya auku ne a shekara ta 2012. Amma bayan shekara biyu sai Zainab ta sake karbar haihuwar irin wannan jaririn, abin da ya bata mamaki.

Duk da yake babu wasu alkaluman adadin 'yan kasar Kenya da ke da wannan matsala ta mata-maza, amma likitoci suna ganin batun bai zarce na sauran kasashe ba - watau kashi 1.7 cikin dari na dukkan mutanen kasar.

Zainab ta bayyana cewa, "A wannan karon, uwar jaririn guduwa ta yi ta bar ni da shi, bata bukaci da in kashe shi ba."

Kamar yadda ta yi a baya, sai Zainab ta kai wannan jaririn gidanta inda shi ma ta raine shi kamar nata. Amma mijinta - wanda masunci ne a tafkin Victoria - bai so haka ba.

"Idan bai yi kamun kifi mai yawa ba, sai kawai ya ce laifin wadannan yaran ne," in ji Zainab.

Hakkin mallakar hoto Charlotte Edey

Charlotte Edey

"Ya kan ce sun jawo mana tsinuwa. Kuma ya bani shawarar da in mika masa yaran don ya hallaka su a cikin tafkin. Amma ban yarda ba. Kuma na fada masa cewa ba zan taba yarda da wannan shawarar ba. Da ga nan sai ya yi fushi - lamarin da yasa muka rika yin fada ko yaushe."

Halin mijin Zainab ya dame ta matuka, saboda haka sai ta yanke hukuncin ta rabu da shi, kana ta tafi da yaran tare da ita.

Zabi ne mai wahala a gare ni domin na saba da rayuwar jin dadi tare da mijina kuma muna da manyan 'ya'ya tare da shi, har da jikoki. Amma ba zan iya jure irin wannan rayuwar ba - ga tashin hankali ga yawan fada. Dole tasa na gudu."

Hakkin mallakar hoto Charlotte Edey

Haihuwa na sauyawa a Kenya. Yawancin mata yanzu a asibitoci suke haihuwa, ba a gida ba. Amma a da unguwar zoma ne kawai aka dogara da su a lokutan haihuwa, kuma akwai wata boyayyar yarjejiniya ta yadda ake yi ma jarirai mata-maza.

"Kashe su suke yi," inji Seline Okiki, wadda ita ce shugabar kungiyar masu aikin unguwar zoma, watau Ten Beloved Sisters, daga yammacin Kenya.

Tsarin shi ne kada a bar jaririn ma ya rayu har ya yi kuka.

Anjeline Naloh, Unguwar Zoma

"Idan aka haifi jariri mata-maza, kawai ana ganin batun na tsinuwa ne kuma ba a kyale jaririn ya rayu. A kan sa ran cewa unguwar zomar ce za ta kashe jaririn kuma ta sanar da uwar cewa bai zo da rai ba."

A yaren Luo, akwai wani shagube na yadda ake kashe irin wannan jaririn. Unguwar zoma su kan ce sun "karya dankali". Wannan yana nufin sun yi amfani da dankali mai karfi wajen yi ma kan jaririn mummunar illa.

"Ba a ba iyayen jariran zabi," in ji sakatariyar kungiyar Anjeline Naloh. "Tsarin shi ne kada a bar jaririn ma ya rayu har ya yi kuka."

A halin yanzu kungiyar ta Ten Beloved Sisters ta bar ma ma'aikatan asibiti karbar haihuwa. Kungiyar ta koma tana tallafa wa mata masu juna biyu da masu haihuwar farko game da illolin kamuwa da cutar HIV.

Amma a lungunan kasar inda babu asibitoci, unguwar zoma ke karbar haihuwa, kuma kungiyar Ten Beloved Sisters na ganin har yanzu ana kashe jarirrai mata-maza.

"Batun boyayye ne. Ba kamar da ba," in ji Anjeline Naloh.

"Har yanzu wadannan abubuwan na faruwa, amma sun zama sirri yanzu," in ji Seline Okiki.

Hakkin mallakar hoto Charlotte Edey

Labarai masu alaka