Shin fitowar Buhari za ta sauya al'amura a Nigeria?

Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu

A ranar Jama'a ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya fito bainar jama'a a karon farko a cikin mako biyu bayan da kasar ta cika da rade-radin cewa rashin lafiyar da ke damunsa ya yi tsanani.

Shugaban na Najeriya, wanda sau uku yana kaurace wa taron Majalisar Ministoci na mako-mako da ake yi kowacce Laraba, ya halarci sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa.

Gabanin fitowar tasa, fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar da ke cewa Shugaba Buhari ba zai gana ba da takwaran aikinsa na Jamhuriyar Nijar, Muhammadou Issoufou, wadda tun farko aka tsara za a yi ranar Juma'ar.

Sanarwar, wacce mai magana da yawun Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce an soke ganawar ne a bisa bukatar Shugaba Issoufou.

Sai dai mutane da dama na ganin an dage ganawar ne saboda rashin lafiyar da Shugaba Buhari ke fama da ita, musamman ganin cewa a harkar diplomasiyya, ya kamata a ce sanarwa irin wannan ta fito daga fadar shugaban Jamhuriyar Nijar.

A da dai, yana halartar zaman Majalisar Ministoci na mako-mako da kuma sallar Juma'a inda abokansa ke samu su gaisa da shi.

Amman bayan ya kasa halartar zaman majalisar na ranar Larabar makon jiya, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya shaida wa manema labarai cewar bisa shawarar likitocinsa, Buhari zai yi aiki daga gida a ranar, kuma ya nemi a kai masa fayel-fayel din da ke bukatar ya yi aiki a kansu gida.
Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Shugaba Buhari ya ce bai taba fama da rashin lafiya irin wannan ba

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"

5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"

28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba

3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne ya rike kasar lokacin da Shugaba Buhari ya yi jinya a London

Gabanin fitowar shugaban kasar zuwa sallar Juma'a, wasu fitattun 'yan kasar da kuma kungiyoyin farar hula sun yi ta kiraye-kiraye a kan ya fito ya gaya wa 'yan kasar hakikanin halin da yake ciki.

Fitaccen marubucin nan da ya ci kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, da ma wadansu shugabannin kungiyoyin farar hula da suka hada da shahararren lauyan nan Femi Falana, da mai fafutukar dimokuradiyya Farfesa Jibrin Ibrahim, sun bayyana cewa ana samun kalamai masu cin karo da juna daga masu taimaka wa shugaban kasar a kan yanayin rashin lafiyarsa, lamarin da suka ce ke kara jefa 'yan kasar cikin fargaba.

A cewarsu, hakan ne ya sa suke yin kira ga Shugaba Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa ya tafi hutun neman magani.

Gwamnatin kasar ta fitar da bayanai kadan game da lafiyarsa, kuma babban jami'in tsaron shugaban kasa ya kori wani dan jarida da ke aiki a daya daga cikin manyan jaridun kasar bayan ya rubuta labari a kan damuwar ta baya-bayan nan.

Masu taimaka wa Buhari kan watsa labarai sun nisanta kansu daga matakin da jami'in ya dauka, kuma sun sa wani babban jami'i ya soke korar da aka yi wa dan jaridar.

Wakilin BBC, Haruna Tangaza, wanda ya halarci sallar Juma'a tare da Shugaba Buhari, ya ce ko da yake shugaban ya dan rame, amma yana magana da tafiya ba tare da wata matsala ba.

Shugaban na Najeriya, wanda ya koma kasar a watan Maris bayan jinyar da ya yi ta kwana 51 a birnin London, ya ce bai taba fama da rashin lafiya kamar wannan karon ba.

A wancan lokacin, ya ce yana samun sauki sosai, "amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti".

Fadar shugaban kasar kuma ta ce shugaban zai ci gaba da gudanar da aiki kadaran kadahan, daidai yadda zai iya har ya samu sauki gaba daya.

Da alama dai fitowar da Shugaba Buhari ya yi sallar Juma'a ta sanyaya ran 'yan kasar, wadanda kafin wannan lokacin ba su san zahirin halin da yake ciki ba.

Sai dai ba a sani ba ko hakan zai rage kiraye-kirayen da wasu ke yi na ganin ya fadi ainihin halin da yake ciki ko kuma kiran da suke yi masa ya koma asibiti domin samun kolawa sosai.

Labarai masu alaka