CBN ya dage haramcin ba da kudin shigo da wasu kaya

Dalar Amurka da kudin Naira na Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dage haramcin yawan kudin da CBN zai iya bai wa 'yan kasuwa na da alfanu in ji masana

Babban Bankin Nijeriya CBN ya ɗage haramcin da ya sa na bai wa wasu ƙananan 'yan kasuwa canjin dala don shigar da wasu kayayyaki daga waje.

Matakin dai zai rage wa ƙananan kamfanoni wahalhalu saboda za su iya samun canjin dala a farashi ƙasa da yadda bankunan kasuwancin ke ba su, a cewar wani masanin tattalin arziƙi, Abubakar Aliyu.

''Ƙananan masana'antu za su samu damar shigar da kayayyakin da za su taimaka musu wajen sarrafa abubuwan da suke samarwa a cikin gida," in ji masanin.

Ya kuma ce ta hanyar ɓullo da tsare-tsare na gajere da matsakaicin zango, kasar za ta iya samun ci gaba kuma za a ga alfanun abin.

Kananan masana'antu suna fuskantar wahala wajen samun kayan aiki da dalolin da suke buƙata don sayo kayan da suke sarrafa hajojinsu.

Masana da dama sun ce idan aka taimaka wa ƙananan masana'antu, da haka za su ci gaba da aiki, mutane za su samu aikin yi, kuma tattalin arziki zai bunƙasa.

Abubakar Aliyu ya ce idan aka ci gaba da wannan tsari ba shakka Nijeriya za ta amfana sosai, haka su ma jama'a, da shi kansa CBN.

A cewarsa, matakin zai kuma saukaka matsalar samun daidaituwar farashin dala, saboda ba lallai ne kuma sai masu masana'antu sun je kasuwar bayan fage ko kuma bankunan kasuwanci suna wahala ba.

Labarai masu alaka