Hodar kwalliya ta haifar wa da wata mata cutar kansa

Talcum powder Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Johnson & Johnson ya ce shaidun kimiyya sun goyi bayan amincin da hodar ke da shi

Wata kotun Amurka ta umarci kamfanin hada magunguna na Johnson and Johnson ya biya wata mata diyyar sama da dala miliyan 100 bayan ta kamu da cutar daji.

Matar dai ta kamu da cutar kansar mahaifa bayan amfani da nau'in hodar kamfanin na Johnson and Johnson.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba, ta riƙa shafa hodar ƙwalliya irin ta mata tsawon sama da shekara goma.

Masu shigar da ƙara a jihar Missouri sun ce kamfanin bai yi wa masu amfani da irin wannan kaya ciki har da hodar jarirai da ke da alaƙa da ma'adanin talcum, cikakken gargaɗi kan hatsarin da ke tattare da shi na cutar kansa ba.

Kamfanin Johnson and Johnson ya ce zai ɗaukaka ƙara.

Shari'ar ta baya-bayan nan na cikin jerin ƙararrakin da aka kai kotunan Missouri game da amincin da kayayyakin Johnson and Johnson masu ma'adanin talcum ke da shi.

Da dama a cikin shari'o'in sun kai ga biyan diyyar maƙudan miliyoyin daloli, ko da yake a watan Maris, wata kotu ta yanke hukuncin da ya bai wa kamfanin nasara.