BH: An kai hare-haren ƙunar-baƙin-wake Konduga

Jami'an ba da agaji
Image caption A lokuta da dama jami'an ba da agaji ne suke kwashe gawawwaki da kuma mutanen da aka raunata don kai su asibiti

Bayanai daga garin Konduga a arewa maso gabashin Nijeriya sun ce wasu 'yan ƙunar-baƙin-wake sun kashe aƙalla mutum huɗu a wasu hare-hare da suka kai cikin daren Alhamis.

Hukumomi dai tukun ba su riga sun tabbatar da kai hare-haren ba.

Wani shaida kuma jami'in sintiri a yankin ya faɗa wa BBC cewa mata biyu ne suka kai hare-haren, don kuwa sun ji ƙarar tashin bam guda biyu.

"Mun ga kan ɗaya haka. Wadda ta zo da bam ɗin mun ga kanta. Ɗayar ma mun ga kanta, bam guda biyu ne ya tashi."

Ya ce an kai hare-haren ne da ƙarfe 11 na dare a wani yankin cikin garin Bulameri.

"A Ƙofar gida ne, a ƙofar gida ne haka, a majalisa. Kuma akwai na cikin gida ma. Yawwa, a waje biyu abin ya tashi, in ji shi."

"Mata guda biyu. Suka zo suka kama hannun wata yarinya tana ihu 'ku sake ni' lokacin kuma dare ya ɗan fara yi, to sai ɗayar ta gudu, saura kuma suna hira sai ta shiga tsakaninsu dumm!

(Mutane) guda hudu Allah ya yi musu cikawa. Guda hudu kuma suka ji rauni."

Ya ce akwai ƙarin mutum ɗaya wanda da bam ɗin da ya tashi, wuta ta kama, ya samu ƙuna.

Masu raunin suna can, ana ƙoƙarin kai su asibiti wayewar garin Juma'a, in ji shi.

Ya ce jami'an tsaro sun je sun ga abin da ya faru kafin su sake komawa wuraren aikinsu a bayan gari.

Labarai masu alaka