An bai wa jam'iyyar Labour ruwa a zaɓen Burtaniya

Kansilolin Conservative
Image caption Kansilolin jam'iyyar Conservative a gundumar Warwick na murnar lashe zaɓe

Sakamakon farko-farko na zaben gundumomi a Burtaniya ya nuna cewa jam'iyyar Conservative mai mulki na samun gagarumar nasara idan an kwatanta da babbar abokiyar hamayyarta, Labour.

Conservative ta ƙwace iko da gunduma biyar, yayin da Labour ta rasa gunduma biyu a sakamakon ƙananan hukumomi da na magadan garin da aka fitar ya zuwa yanzu.

Daga cikin gundumomin da jam'iyya mai mulki ta samu har da Lincolnshire inda jam'iyyar UKIP wadda ke kan gaba a fafutukar Burtaniya ta fita daga Tarayyar Turai, ta yi asarar duk kujerunta.

Wani ƙusa a jam'iyyar ya bayyana sakamakon a matsayin "mai ban takaici matuƙa".

Jam'iyyar Labour ta rasa gundumar Blaenau Gwent da ta Bridgend.

Sakamakon Liberal ya zo a ciccire ya zuwa yanzu, ko da yake ta gaza hana Conservative karbe gundumar Somerset.

Ana sa rai zaɓukan na majalisun ƙananan hukumomi da magadan gari za su fitar da wata ƙwaƙƙwarar manuniya kan yadda babban zaɓen Burtaniya na watan gobe zai kasance.

Wani ƙwararre kan harkokin siyasa, Farfesa John Curtice ya ce "Tabbas ɗan sakamakon da muka samu a cikin dare, mun ga yadda al'amura suka sauya.

Conservative ta bai wa jam'iyyar Labour ruwa da kimanin kashi bakwai cikin 100, hakan ya nuna cewa Conservative ta sha gaban Labour a fadin ƙasar idan an kwatanta da shekara ta 2013"

Nan gaba a Juma'ar nan ce za a fitar da mafi yawan sakamako a yankunan Ingila da Scotland da kuma Wales.

Labarai masu alaka