Shugaban Niger ya ɗage ganawarsa da Buhari

Buhari da Issoufou Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin biyu sun taba ganawa a can baya

An soke wata ziyara da shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou ya shirya kai wa Najeriya don ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce an soke ganawar ne a bisa bukatar shugaba Issoufou din.

Ya kara da cewa shugaba Issoufou ya ce yana da wani al'amarin mai matukar muhimmanci da ya kamata ya tsaya ya aiwatar a kasarsa.

Sanarwar ta ce tun da fari an kammala duk wani shiri a fadar shugaban Najeriya na tarbar Mista Issofou da tawagarsa.

"An shirya cewa shugabannin biyu za su halarci sallar Juma'a tare da kuma cin abincin rana, kafin daga bisani a soke ziyarar," in ji sanarwar.

Mista Adesina ya ce za a sanar da wata sabuwar ranar da shugabannin za su gana da zarar shugaba Issoufou ya sake sanar da hakan.

A wannan makon ne dai ce-ce-ku-ce kan halin da lafiyar shugaba Buhari ke ciki ya kara yawa, saboda rashin halartar taron majalisar ministocin gwamnati da bai yi ba a ranar Laraba a karo na uku a jere.

Sai dai ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce shugaba Buhari bai halarci taron ba ne saboda yana ci gaba da hutawa kamar yadda likitoci suka ba shi shawarar yi.

Kaza lika wasu manyan jami'an gwamnatin kasar sun ce shugaban yana nan lafiya don har sun gana da shi sun kuma tattauna kan abubuwan da suka shafi ci gaban kasa.

Labarai masu alaka