Nigeria: Yadda tsarki da sabulu ya jawo wa wata mace matsala

Wanke al'aura

Da yawan mata na tunanin wanke al'aura da sabulu ko wasu sinadarai abu ne da yake da muhimmanci sosai, musamman don tsaftace wajen da a ko yaushe yake a rufe. Sai dai hakan ya yi muguwar illa ga wata mata a Najeriya.

Wannan dai al'ada ce da ta gama gari, alal misali, kiyasi ya nuna cewa kashi 20 zuwa 40 cikin 100 na matan Amurka da ke tsakanin shekara 15 zuwa 44 suna yawan wanke al'aurarsu da sabulu ko wasu sinadaran daban.

Duk da cewa a Najeriya babu wata kididdiga da ke nuna adadin matan da ke irin wannan abu, amma akwai tabbacin cewa al'ada ce da mafi yawan matan kasar ke yi don tsaftace kansu. Sai dai abin da yawancin mata ba su sani ba shi ne, hakan na da illa sosai ga lafiyarsu.

Hajiya Ladidi, wacce muka sauya wa suna, ta shaida min irin yadda yin tsarki da sabulu ya yi mata muguwar illa ga lafiyarta.

"Na kasance mace mai yawan son tsafta da kamshi, don haka ko yaushe cikin wanke tare da kalkale jikina nake musamman al'aura, wacce nake ganin rashin kula da ita na iya sa a dinga jin dan wari-wari na tashi".

Ta ce ta kan shafe kusan sa'a daya a bandaki idan ta shiga wanka, "don ina ɓata lokaci sosai wajen wanke al'aurata da sabulai kala-kala". Sannan tana fesa turaruka kala-kala.

"A duk yayin da na kammala al'ada kuwa to gyaran yana fin haka don har tsiyaya turaren miski nake a al'aurar tawa mai yawa ba dangwalawa a auduga ba, don ina son gyaran nawa ya fi na kowa."

Sai dai ba a dade ana tafiya ba, sai ta fara ganin ba daidai ba, inda ta fara da "zubar wani ruwa kalar madara daga al'aurata", inda har ta "kafafuna yake zirara da yake ban faye sa ɗan kamfai ba (Pant)".

"Wasa-wasa sai ga shi ya fara wari sosai ya kuma sauya kala zuwa kore-kore. Wani lokacin sai na dinga tsarguwa ko wanda ke zaune kusa da ni ma na iya jin warin.

Ladidi ta kara shiga cikin damuwa tana tunannin ko cuta ta dauko wajen amfani da ban-dakin da ba shi da tsafta a wani wajen.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata sun yi fice wajen son yin kwalliya

"Don haka sai na fara tambayar mutane sai wasu su ce ko mijina ne ya kwaso cuta wajen matan banza ya shafa min, ni kuma can cikin raina gaskiya na yarda cewa mijina ba ya neman mata.

"A karshe dai na je asibiti a ka duba ni sai likitan ya bani gwajin ciwon suga don larurar tawa na daga cikin alamunsa, amma da sakamako ya fito sai a ka ga ba haka ba ne.

Daga nan sai aka tura ta wajen wata ƙwararriyar likitar mata a National Hospital da ke Abuja, inda ta ce tambaye ta ko akwai abin da nake yawan sawa a al'aurata.

A nan na ta shaida mata ba na ta komai amma tana son tsafta kuma ta kan wanke shi da duk wani sinadari da ake sayarwa don wajen ya yi kamshi.

A lokacin ne likita ta shaida mata cewa lallai wadannan abubuwa su suka yi min illa.

Ta sa ta tayi gwaje-gwaje da dama har da gwajin mahaifa na Pap Smear, inda aka gano kwayoyin cuta sun "kama ƙashin ƙugunta wanda aka fi sani da Pelvic Inflammatory Disease, hakan kuma na iya toshe mahaifa daga ɗaukar ciki.

"A ƙarshe dai ta ɗora ni a kan magunguna da allurai na musamman har tsawon wata biyu, aka kuma sake wasu gwaje-gwajen a ka gano cewa cutar ta tafi. Amma fa na sha wahala gaskiya ba kaɗan ba."

Hajiya Ladidi ta ce min a yanzu haka ba ta wanke al'aurarta da komai da ya wuce ruwa, don kuwa ita ta ga abin da ta gani.

Mene ne 'wanke al'aura' da sinadarai?

Dakta Hauwa Isa Abdullahi wata kwararriyar likitar mata ce, kuma ita ce mai asibitin Get Well a birnin Kano, ta ce "Mata suna yin haka ne da zummar kawar da wari, ko bashi-bashi da ke fita daga al'aura ko kuma wanke wajen tas bayan kammala al'ada ko saduwa."

Image caption Dakta Hauwa Isah Abdullahi ƙwararriyar likitar mata ce a Kano

Mata kan yi amfani da sabulun wanka, ko sinadarin detol ko turare ko wasu sinadarai da yanzu ake sayar da su a kantuna don yin wannan wanki, "Hakan ta sa suke ganin kamar abu ne mai kyau tun da ana sayar da shi ta ko ina," in ji Dokta Hauwa.

"Watakila su kasashen da ke irin wadannan sinadari sun gwada da yanayin jikin matansu ne, sai suka yi sinadaran ta yadda ba za su yi musu illa ba. Don haka kamata ya yi mu ma a ce an yi hobbasar yin bincike don a yi na daidai matan nahiyarmu, yadda ba zai yi musu illa ba.

"Amma gaskiya a yanzu likitoci ba su da tabbacin wadannan sinadarai sun dace da jikin matan nahiyarmu ba, kuma mun ga illar su sau da dama, don haka daina amfani da su shi zai fi alheri."

A bayanin da Dr Hauwa ta yi min, ta ce ita al'aurar mace an halicce ta ne da wasu kwayoyin halitta (vaginal flora) irin wadanda ba a gani da kwayar ido, wadanda aikinsu shi ne su kare wajen daga saurin kamuwa da cututtuka.

Su kuma wadannan kwayoyin halitta ba a so a dinga sa musu wani sinadari mai karfi a wajen don zai kashe su ne, "Da sun mutu kuma, to al'aurar za ta zama ba ta da kariya nan da nan cuta za ta iya shiga wajen," a cewar Dr Hauwa.

Sakamakon hakan cututtuka kala-kala za su iya shigar mace ta al'aurarta, saboda duk wata kariya, karfin sabulu da sinadaran nan sun kawar da ita.

Wadanne cututtuka ne mace za ta iya kamuwa da su?

Likitoci da dama sun bayyana cewa da zarar kwayoyin halittar da ke kare al'aurar mace sun mutu, to za ta iya fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka kamar:


Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata kan iya kamuwa da cututtuka da dama da yawa ba su san illar tsarki da sabulu ba

Cututtukan da mata za su iya fuskanta idan kwayoyin halitta suka mutu

 • Haifar da kwayoyin cuta (Infection) da za su baibaye al'aurar mace wadanda za su iya kara hadarin jawo nakuda tun lokacin haihuwa bai yi ba, da kuma hadarin saurin kamuwa da cututtuka masu alaka jima'i kamar ciwon sanyi da sauran su.
 • Yana iya jawo kwayoyin cuta ga mahaifa da kwayayen haihuwa da aka fi sani da Pelvic inflammatory disease (PID). "Wannan al'amari na iya hana mace samun haihuwa kwata-kwata, ko kuma ya sa mace ta dinga daukar ciki a wajen mahaifa," in ji Dakta Hauwa.
 • Wata mujallar lafiyar mata ta Amurka ta intanet WebMD, ta ce wani bincike da aka yi ya gano cewa mata masu wanke al'aura da sabulu ko sinadarai sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar PID.
 • Akwai kuma yiwuwar mace ta dinga fama da matsanancin kaikayi a gabanta, ko kuraje su fito mata ko kuma al'aurar ta dinga tsagewa.
 • A wasu lokutan wani ruwa mai kauri mai kalar dorawa ko kore mai kuma wari zai ta fitowa daga gaban mace, wanda dole sai ta je asibiti don a magance shi.

Ita ma wata kwararriyar likitar matan a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Hauwa Umar Shu'aibu, ta ce idan mata suna son su kasance da tsaftatacciyar al'aura, to ya kamata su guji 'cusa abubuwa ko wanke wajen da abubuwa ba tare da shawarar likitoci ba.'

'Matsalar na gawurta'

Dr Hauwa Shu'aibu ta ce suna yawan samun irin wadannan matsalolin da dama daga wajen mata.

"Za ki ga mace ta zo tana korafin cewa tana fama da matsalar kaikayi, ko fitar wani ruwa mai wari daga gabanta, idan ki ka bi diddigin lamarin sosai sai ki samu ko dai yawan wanke wajen da sinadarai masu karfi ne ko kuma cusa wasu abubuwa da nufin inganta rayuwar aurenta.

"A sakamakon haka sai ki ga an shiga wani hali da sai an yi ta neman magani don a samu waraka."

Da yake wannan baiwar Allah ta kawo batun amfani da almiski kuma na san akwai hadisin da ya ce, "Nana Aisha R.A ta kan yi amfani da shi a duk lokacin da ta kamala al'ada," hakan ya sa na bijirowa likitocin wannan tambayar.

Dakta Hauwa Abdullahi da Dakta Hauwa Shu'aibu duk suna kan matsaya daya, inda suka ce lallai amfani da almiskin yana da kyau, amma ba zurara shi za a yi cikin al'aurar ba, abin da ake so mace ta yi shi ne ta shafa a jikin dan kamfai dinta (pant) sannan ta sa pan din.

A cewar su idan aka yi hakan ma ya wadatar, kuma an aikata Sunnar da ake so din.

Hakkin mallakar hoto AFP

'Al-miski gangariya'

Sai dai shi kansa batun samun almiski gangariya irin wanda Nana Aisha ta yi amfani da shi akwai ayar tambaya a kansa. Wasu na ganin a yanzu ma samun gangariyar almsika 'Musk Aisha' yana da matukar wahala don shi a kan same shi ne daga jikin maƙoƙon Barewa, kuma yana da matuƙar tsada.

Wata mazauniyar Saudiyya, wacce kuma mu'amalarta da Larabawa ya sa ta san kan turarukansu Khadeejah Ummi Madaki ta ce, Musk Aisha na da wahala ake samun sa, don 'yar mitsitsiyar kwalbar ma kan kai riyal 100, kusan naira 10,000 kenan, kuma ba a ko wanne kanti ake samu ba a Saudiyyar ma.

"Gaskiya yawancin almiskin da ake sayarwa a Najeriya ba mai kyau ba ne, gauraye-gauraye ne kawai na turaruka daban-daban, mata kuma sai su saya su yi ta amfani da shi ba tare da la'akari da illar da zai yi musu ba.

"Don haka ya kamata mata su daina bari ana yaudarar su a kawo ko wanne turare a ce Musk Aisha ne," in ji Khadeejah.


Matakan da za a bi wajen tsaftace al'aura

Daga Dr Hauwa Isa Abdullah da Dr Hauwa Umar Shu'aibu

 • Tsarki da ruwa kawai ba sabulu. Amma Dr Hauwa Isa Abdullahi ta ce, "Kina iya amfani da sabulu kamar na jarirai ki wanke al'aurar sau daya a wata, wato kamar lokacin da ki ka kammala al'ada."
 • Idan kina son tsane wajen bayan kin yi tsarki to kar ki yi hakan da toli-fefe, (toilet paper), zai fi kyau ki tanadi kyalle mai tsafta ki goge da shi.
 • Dr Hauwa Isa ta ce, "Amfani da toli-fefar ba shi da kyau don za ta iya murmushewa ta shige cikin al'aura kuma hakan zai iya sa wa mace kwayoyin cuta. Sannan kuma barin wajen da danshi ma yana iya jawo yaduwar kwayoyin cuta (bacteria).
 • Ka da ki dinga cusa magungunan mata ko turare a al'aurar, idan ma almiskin ne zai fi kyau ki shafa a dan kamfanki kawai.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
 • Ka da ki dinga zama a cikin ruwan dumi da dettol, zai fi kyau ki dinga zuba gishiri a ruwan dumin idan ma kina son zama a ciki ne maimakon dettol. Dr Hauwa Shu'aibu ta ce, "Dettol yana da karfi sosai zai iya kashe kwayoyin halittar da ke al'aurar wadanda suke kare ta daga kamuwa da cututtuka."
 • Yawan sa dan kamfai (pant) yana da muhimmanci, ka da a dinga zama ba pant.
 • Idan kin wanke pant dinki to zai fi kyau ki shanya shi a rana, "Hasken ranar yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta idan har akwai a jikin pant din, shanyawa a bandaki ba shi da amfani," in ji Dr Hauwa Shu'aibu.
 • Yana da kyau bayan pant din ya bushe idan da hali a goge da dutsen guga (Iron).
 • Ki guji sa pant idan bai karasa bushewa ba.
 • Idan kina tsarkin bayan-gari to ki fara gogewa tukunna, sannan sai ki wanke amma ki guji ruwan tsarkin ya taba al'aurarki.
 • Ki dinga amfani da pant mai taushi ba mai santsi ba.
 • Ki yawaita tsarki da ruwan dumi.