Nigeria: Shugaba Buhari ya fito sallar Juma'a

Buhari
Image caption Shugaba Buhari ya gaisa da mutane bayan kammala sallar

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya halarci sallar Jumu'a a masallacin fadarsa da ke birnin Abuja a yau, abin da ya kawo karshen rade-radi da ake yi game da halin lafiyarsa.

Shugaban Buhari ya bayyana a masallacin ne da misalin karfe 1:30 agogon kasar inda ya halarci sallar wadda ta dauki tsawon minti 12.

Ana zuzuta rashin lafiyar mijina — Aisha Buhari

Wane ne Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria?

Wakilinmu da ke masallacin Haruna Shehu Tangaza, ya ce ko da yake akwai alamun rama a jikinsa har yanzu; yana tafiya da kuma magana kamar yadda ya saba lokacin da yake lafiya lau.

"Bayan gama sallar ya dan tsaya ya gaisa da mutane na dan gajeren lokacin kafin ya wuce zuwa gidansa." In ji shi.

Shugaban ya je masallacin ne da misalin karfe 1.30 na rana karkashin rakiyar masu tsaronsa. Ya saurari huduba ya kuma shafe minti 12 cikin masallacin.

Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar da safe na cewa an dage wata ganawar da shugaban zai yi da takwaransa na Jamhuriyar Nijar ta kara ta da shakku kan halin lafiyarsa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buhari ya fito masallacin Juma'a

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da cece-kuce ke cigaba da yin kamari kan halin da yake ciki.

Rashin bayyanarsa wajen sallar a makon jiya ya saka wasu 'yan kasar tunanin halin lafiyarsa ya kara tabarbarewa.

An yi ta ce-ce-ku-ce a kan halin da lafiyar shugaban ke ciki a wannan mako saboda rashin ganin sa a bainar jama'a, inda wasu ke cewa ta yi tsanani sosai har suna kiransa da ya tafi Ingila don sake ganin Likita.

Sai dai wasu manyan jami'an gwamnatin kasar sun karyata hakan, inda suka ce sun gana da shi kan al'amuran da suka shafi kasa, kuma rashin lafiyar ba ta kwantar da shi ba, hutawa kawai yake yi.

Labarai masu alaka